• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, June 5, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Bikin Sallah: Daso ta raba wa mata 60 kyautar atamfofi

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
April 15, 2023
in Labarai
0
Saratu ya tsakiyar matan da ta ba tallafi

Saratu ya tsakiyar matan da ta ba tallafi

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Jaruma a a Kannywood, Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso), ta yi wani namijin ƙoƙari domin tallafa wa mata masu ƙaramin ƙarfi guda 60 inda ta gwangwaje su da turamen atamfa domin su samu abin da za su saka domin yin kwalliyar Sallah.

Ta yi rabon atamfofin a safiyar ranar Asabar, 15 ga  Afrilu, 2023 a wajen taro mai suna Daso Event Centre.

Gidan taron, wanda mallakin ta ne, ya na ‘Yanƙusa, ya na kallon baifas kusa da NNPC a Kano.

Tun da farko da ta ke bayani kan manufar rabon atamfofin, Hajiya Saratu ta ce, “Manufar shirya wannan taron dai shi ne domin mu haɗu da ku mu yi zumunci da kuma ganin juna, kamar yadda ku ke samun labari na ko ku ke gani na a talbijin, domin ni a gaskiya ban taɓa ganin ku ba sai a yanzu da mu ka haɗu, don ba ni na gayyato ku ba, na sa a gayyato mini mata masu buƙatar taimako daga cikin marayu, zawarawa da kuma ‘yan mata. Don haka ba ni da wata sanayya a tsakani na da ku sai yanzu da mu ka haɗu a wannan wajen.

“Saboda haka mu na fatan za mu yi amfani da wannan dama wajen kyautata alaƙa tare da yi wa juna addu’a.”

Daso na miƙa wa wata mata atamfa

Ta ƙara da cewa, “Ganin halin da mutane su ke ciki a wannan lokacin, na yi amfani da ɗan kuɗin da na ke samu a kamfani na na Daso Entertainment na samar da atamfa ta mutane guda sittin don su samu kayan da za su saka a bikin Sallah. Kuma mu na fatan wannan niyyar tamu ta zama mai amfani a gare mu duniya da lahira. 

“Don haka in godiya a gare ku da ku ka samu zuwa domin karɓar wannan kayan tallafi, kuma za mu ci gaba da yin hakan nan gaba kamar yadda mu ke da tsari na ciyarwa da kuma rabon kayayyakin abinci da mu ke yi a birni da ƙauyuka. Da fatan Allah ya mayar da kowa gidan sa lafiya.”

Matan da su ka samu atamfofin sun nuna farin cikin su tare da godiya, da kuma addu’a ga Daso kan manufar ta ta taimakon masu ƙaramin ƙarfi.

Daso da mata mabuƙata a wajen taron
Hajiya Saratu tare da ma’aikatan ta, a bayan su kuma matan aka yi wa kyautar atamfofi

Loading

Tags: atamfar SallahSaratu Giɗaɗo Dasotallafi
Previous Post

Sharhin littafin ‘Jiki Magayi’

Next Post

Lauyoyi a Kano sun kai kukan su ga sarakunan Jihar Katsina kan ‘waƙoƙin ɓatanci’ na Rarara

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post
Dauda Rarara

Lauyoyi a Kano sun kai kukan su ga sarakunan Jihar Katsina kan 'waƙoƙin ɓatanci' na Rarara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!