FITACCIYAR jaruma Ummi Ibrahim (Zee-Zee) ta bayyana cewa ta shiga ƙuncin rayuwa, har ta na jin kamar ta kashe kan ta.
Kyakkyawar jarumar ta faɗi haka ne a wani saƙo da ta wallafa a Instagram a yau da yamma.
A saƙon, wanda ta rubuta da Turanci, jarumar ta Kannywood ta ce: “This days i live a MISERABLE life to the extend that I want to commit SUICIDE ,but please non of any body should ask me why ? All I need from you people is a PRAYER !”
Mujallar Fim ta fassara rubutun kamar haka: “A ‘yan kwanakin nan na shiga matsanancin ƙuncin rayuwa, ta yadda har na kan ji ina so na kashe kai na. Amma don Allah kada kowa ya tambaye ni dalili. Abin da kawai na ke buƙata a gare ku jama’a shi ne ADDU’A!”
Jarumar ta yi amfani da manyan haruffa wajen rubuta wasu daga cikin kalaman nata.
Ummi dai ta kasance ɗaya daga cikin jaruman finafinan Hausa da tauraron su ya haska a farkon jerin shekarun 2000.
Ta fito a manyan finafinai da dama irin su ‘Jinsi’, ‘Gambiza’ da ‘Tutar So’.
Haka kuma ta taka rol sosai tare da manyan jarumai irin su Ali Nuhu, marigayi Ahmed S. Nuhu, Abba El-Mustapha da Ibrahim Maishunku.
A jarumai mata kuma ta yi tashe da irin su Jamila Nagudu, Farida Jalal, Ummi Nuhu, Hafsat Shehu da Rasheeda Adamu Abdullahi, Ruƙayya Dawayya da Mansura Isah.
Sai dai daga baya an daina jin ɗuriyar ta na tsawon wasu shekaru da dama a industiri, lamarin da wasu su ke ganin ya sa tauraron ta ya dusashe.

A nazarin da mujallar Fim ta yi wa irin saƙonnin da jarumar ta riƙa turawa a Instagram cikin ‘yan kwanakin nan, ba ta ga wani abu mai nuna damuwa game da ita ba.
Mujallar ta dai lura da yadda Zee-Zee ke matuƙar son shahararren mawaƙin nan marigayi Michael Jackson domin kuwa daga Nuwamba 2020 zuwa jiya ta tura hotunan sa har guda 12 tare da kalaman shauƙi da yabo.
Ɗimbin mabiyan jarumar sun yi mamakin saƙon da ta wallafa da yammacin ranar nan, tare da kira a gare ta da ta ɗauki haƙuri kuma ta maida komai nata ga Allah (swt).
Akwai kuma waɗanda su ka tunatar da ita cewa hukuncin wanda ya kashe kan sa shi ne wutar Jahannama, don haka kada ta kuskura ta aikata abin da ta ke tunanin aikatawa.
Hasina Ɗan-Chaina, wadda ƙanwar Ummi Zee-Zee shaƙiƙiya ce, ita ma ta bayyana mamaki game da wannan abu da yayar tata ta yi tare da kira a gare ta da ta gaggauta goge shi.
Hasina, wadda ke auren fitaccen attajiri kuma ɗan siyasar nan mazaunin Jos, Alhaji Abdullahi Adamu Ɗan-Chaina, wanda ya taɓa takarar zama gwamnan Jihar Bauchi, ta faɗa wa Zee-Zee a Instagram cewa: “Subhanallah why this pls kuma on social media tnk god kina da rai kina da lfy mama is alive ci da sha baba ya bar miki rufin asiri na gidan duniya dai pls delete this post now now now.”
Mahaifin su Zee-Zee dai ya rasu ne shekaru huɗu da su ka gabata, amma mahaifiyar su na nan da ran ta kamar yadda Hasina ta yi ƙoƙarin nuna wa yayar tata.
Ya zuwa lokacin rubuta wannan labari, mujallar Fim ta karanta martani kimanin 170 da mabiyan Zee-Zee su ka yi a ƙarƙashin saƙon nata a Instagram.
Zee-Zee, wadda ta aika saƙon tare da hoto mai bayyanar da tsananin damuwa a fuskar ta (ga shi nan a tare da wannan labarin) ba ta dai goge saƙon ba kamar yadda Hasina ta buƙace ta ta yi.







