• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Zee-Zee: An damfare ni N450m, shi ya sa na so kashe kai na

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
April 4, 2021
in Labarai
0
Zee-Zee: An damfare ni N450m, shi ya sa na so kashe kai na
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCIYAR jaruma Ummi Ibrahim (Zee-Zee) ta bayyana wata damfarar ɗaruruwan miliyoyin naira da ta ce an yi mata a matsayin dalilin da ya sa ta ke son ta kashe kan ta.

A wani saƙon murya da ta fitar a yammacin wannan rana, Zee-Zee ta ce wani Inyamiri ne ya damfare ta zunzurutun kuɗi har naira miliyan 450 a kan harkar ɗanyen mai, shi ya sa ta ji gaba ɗaya ma zaman duniyar ya ishe ta.

Bayan sallama da ta yi tare da bayyana cikakken sunan ta, ta fara da cewa, “Na yi wannan ‘voice note’ ɗin nan zuwa ga ‘yan’uwa na ‘yan fim, ma’ana ‘yan Kannywood, domin in miƙa gaisuwa ta da kuma godiya ta ta musamman gare ku ga ƙauna da ku ka nuna min dangane da iftila’in da ya faɗa min a wannan satin, wanda har ta kai ga rai na ya ɓaci, shaiɗan ya shiga zuciya ta, na yi kuma iƙirarin zan kashe kai na.

”To gaskiya abin da ya sa na faɗi cewa zan kashe kai na shi ne Musulma ce ni, na yarda da ƙaddara mai kyau da mara kyau, amma akwai ƙaddarar da idan mara kyau ce bawa ya na rasa tunanin sa; to ni ƙaddarar da ta same ni ita ce akwai wani wanda mu ka yi kasuwanci da shi, Inyamuri ne a Jihar Lagos, mun yi kasuwanci a kan abin da ya shafi ɗanyen mai wanda zan sara a gurin sa in sayar in samu riba. Sai na tattara kuɗi na, wato dala, na ba su shi masu yawa, amma kuma in an canza kuɗin zuwa kuɗin Najeriya zai tashi zuwa miliyan ɗari huɗu da hamsin.

“To shi ya sa gaskiya da na fahimci damfara ta ya yi sai na ji kawai na rasa tunani na, ina so in ma kashe kai na. Subhanallah! Amma dai alhamdu lillah hakan bai samu ba, Allah ya ƙwace ni.

Ummi Ibrahim (Zee-Zee): “Shaiɗan ne ya shiga zuciya ta”

”To wannan shi ne dalilin da ya sa na furta kalamin zan kashe kai na, wanda kuma ko da gwamna ne aka masa irin wannan damfarar dole zai girgiza ballantana ni ‘yar kasuwa.”

Ta ƙara da cewa, ”Alhamdu lillah, hankali na ya dawo jiki na, ƙudiri na na kisa da na ce zan wa kai na na janye shi da taimakon Allah da kuma addu’ar ku, ku masoya na ‘yan Kannywood da kuma ahali na, wato ‘family’ da abokai na da kuma wasu daga cikin waɗanda na ke kasuwanci da su.

”Saboda haka lafiya ta ƙalau, ina nan Lagos. Don haka duk wanda ya nuna damuwar sa da alhinin sa zuwa gare ni na gode muku sosai. Allah ya saka da alheri. 

“Kuma har ga Allah ban san haka abokan sana’a ta ‘yan fim su ke ƙauna ta ba sai da wannan abin ya faru da ni shi ne kowa ya dinga nuna damuwar sa, ana ta yi min waya da saƙonni. Sai na yarda ku na ƙauna ta. 

“Kuma na gode da irin ƙaunar. Ni ma kuma ina ƙaunar ku. Allah Ubangiji ya bar mu tare ya kuma haɓɓaka mana masana’antar mu ta Kannywood, ya sa ta zama a jerin manyan masana’antun shirya fim na duniya in dai za a yi magana ita ma a sa da ita.”

Har wa yau Zee-Zee ta gode wa jaruma Rasheeda Adamu Abdullahi, inda ta ce ita ce mutum ta farko da ta fara yi mata waya ta jajanta mata, “sannan kuma ki ka  umarce ni da na tura wa ‘yan’uwa na abokan sana’ar mu ‘yan fim domin su tabbatar da ina cikin ƙoshin lafiya. Na gode, Allah ya saka da alkhairi. Ku huta lafiya.”

In dai za a iya tunawa, a jiya ne mujallar Fim ta kawo maku labari a kan yadda Zee-Zee ta fusata ta wallafa a shafin ta na Instagram cewa, “A ‘yan kwanakin nan, na shiga matsanancin ƙuncin rayuwa, ta yadda har na kan ji ina so na kashe kai na. Amma don Allah kada kowa ya tambaye ni dalili. Abin da na ke buƙata a gare ku kawai shi ne addu’a.”

Rubutun nata ya jawo ka-ce-na-ce a soshiyal midiya, inda a yayin da wasu ke ba ta haƙuri tare da nasiha, wasu kuwa ƙaryata ta su ke yi, su na faɗin neman suna ne kawai ta ke yi saboda an daɗe ba a ji ɗuriyar ta a Kannywood ba.

Tags: depression in Nigeriahausa actresshausa filmsKannywoodUmmi Zee-Zee
Previous Post

Cewar Zee-Zee: Ku sa ni a addu’a, ji na ke kamar in kashe kai na

Next Post

Tsakanin shahara da jarraba

Related Posts

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry
Labarai

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry

June 15, 2025
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
Next Post
Tsakanin shahara da jarraba

Tsakanin shahara da jarraba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!