ALLAHU Akbar! Furodusa a Kannywood kuma mawallafin mujallar Gambiza, Alhaji Nasiru Anchau, ya yi rashin mahaifi.
Alhaji Ɗanjuma Haruna Anchau ya rasu da misalin ƙarfe 5:00 na asuba a jiya Litinin a gidan sa da ke Titin Alƙali, a cikin garin Anchau Takalafiya, Jihar Kaduna.
An yi sallar jana’izar dattijon mai kimanin shekaru 120 da misalin ƙarfe 10:30 na safe a ƙofar gidan sa.
Marigayin a lokacin rayuwar sa, ya yi malamin makarantan boko, kuma ya yi sakatare ga Sarkin Zazzau, marigayi Dakta Shehu Idris.
Ya rasu ya bar ‘ya’ya 14, maza 8, mata 6. Nasiru, wanda mazaunin Kaduna ne, shi ne babba a cikin su.
Allah ya jiƙan sa, ya albarkaci dukkan abin da ya bari, amin.
![]()







