HUKUMAR Kare Haƙƙin Masu Mallaka Da Yaƙi Da Satar Fasaha ta Ƙasa (NCC) ta nemi haɗa hannu da Hukumar Tace Finafinai Da Ɗab’i ta Jihar Kano domin wayar da kan abokan hulɗar ta kan sababbin dokokin hukumar waɗanda aka yi wa gyara.
Hakan ya biyo bayan ziyarar da NCC ta kai wa hukumar a Kano a ranar Talata.
Da yake jawabi a yayin ganawa da manema labarai, Alhaji Sani Ahmad, wanda shi ne mai kula da jihohin Kano, Katsina da Jigawa na hukumar, ya ce ya ziyarci Hukumar Tace Finafinan ne domin neman goyon bayan su ta yadda za su haɗa hannu kan wayar da kan abokan hulɗar su, musamman masu sana’ar waƙa, marubuta, masu shirya finafinai da masu fassara finafinai daga zuwa Hausa kan sababbin tanade-tanade da sabuwar dokar da hukumar ta yi dangane da yadda za su gudanar da ayyukan su.
Alhaji Sani ya ƙara da cewa doka ta ba wa hukumar su damar lura da ayyukan masu wannan sana’a tare da hukunta su yayin da aka same su da laifin karya dokokin ta.

A nasa jawabin, Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, ya gode wa jami’an hukumar NCC ɗin game da girmama hukumar sa da su ka yi na kawo ziyara ta musamman domin ƙulla alaƙar aiki tare da kawo hanyar da za a ciyar da abokan hulɗar hukumomin nasu gaba.
El-Mustapha ya yi alƙawarin bai wa hukumar cikakken haɗin kai tare da goyon baya ta yadda za a cimma nasarorin ayyukan da aka sa a gaba.
Ya ce a kowane lokaci ƙofar sa a buɗe ta ke domin haɗin gwiwa da taimakawa.