ALLAHU Akbar! A safiyar Litinin, 22 ga Agusta, 2022 Allah ya ɗauki ran matar fitaccen darakta kuma furodusa mazaunin Zariya, Alhaji Magaji Sulaiman, mamallakin kamfanin shirya finafinai na Sulson.
Hajiya Hannatu Yahaya ta rasu da misalin ƙarfe 6:00 na safiya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Shika, Zariya, sakamakon doguwar jinya da ta sha fama da ita.
Marigayiyar, mai kimanin shekara 44 a duniya, ta rasu ta bar mijin ta Alhaji Magaji da kuma ‘ya‘ya biyar.
An yi jana’izar Hajiya Hannatu da misalin ƙarfe 2:00 na rana a gidan mijin ta da ke Unguwar Zariya, a cikin garin Zariya, sannan aka kai ta gidan ta na gaskiya a maƙabartar da ke kusa da gidan Alhaji Magajin.
Wasu daga cikin ‘yan fim da su ka halarci jana’izar sun haɗa da Malam Musa Muhammad Abdullahi, Cash Man, Dikko Yakubu, Ibrahim Ɗandolo, Buhari Maizago, Abdullahi Korau, Na’atala Zariya da sauran su.
Allah ya rahamshe ta, ya albarkaci dukkan abin da ta bari, amin.