FITACCEN jarumi kuma furodusa T.Y. Shaban ya mayar da martani ga ‘yan fim masu zargin cewa shi da jarumi Shariff Aminu Ahlan (‘Jinsee’) sun laƙume tallafin da ɗan siyasar nan na Kano mai suna A.A. Zaura ya yi alƙawarin bai wa Kannywood, ya ce sam ba haka ba ne.
Shaban ya nuna cewa tallafin bai shigo hannun su ba.
A.A. Zaura ya tsaya takarar zaɓen fidda gwani na zama gwamnan Kano a jam’iyyar APC, inda daga nan kuma ya yi takarar tsayawa zaɓen sanata. Mutum ne wanda ke raba kayan agaji ga ƙungiyoyi daban-daban a jihar.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba da labari jiya cewa wasu ‘yan fim su na zargin jaruman biyu da yin sama da faɗi da tallafin da ɗan siyasar ya taɓa alƙawari a wajen wani babban taro cewa zai bayar.
Zargin ya shigo ne ganin cewa sun ji shiru game da alƙawarin da aka yi da daɗewa, ga shi kuma ya na ta raba tallafi ga wasu ƙungiyoyin a Kano.
Shaban da Ahlan dai su ne shugabannin wata ƙungiya mai suna ‘Kannywood Celebrity Forum’ ko ‘KCF4AAZAURA’ a taƙaice, wadda su ka kafa don ƙarfafa lamirin A.A. Zaura a cikin ‘yan Kannywood.
Buga labarin da wannan mujallar ta yi jiya ya sa ‘yan fim da dama sun yi kira ga jaruman biyu da su fito su kare kan su, maimakon su yi gum da bakin su kamar yadda su ka yi lokacin da wakilin mu ya waiwaye su kan zargin.
A martanin da ya aiko wa da mujallar Fim a rubuce a daren jiya, wadda kuma ya raba wa ƙungiyoyin da ke cikin Kannywood, TY Shaban ya ce: “Kannywood Celebrity Forum (KCF4AAZAURA) wata ƙungiyar ce da suka ƙirƙira domin kawo sauyi a masana’antar Kannywood a tafiyar siyasar Jihar Kano da ma Nijeria baki ɗaya bisa haɗin kan wasu jarumai, mawaƙa, ‘yan ‘comedy’, mawallafa har da masu ruwa da tsaki a harkokin finafinai domin kawo cigaba ta hanyar samar da abubuwan cigaba a Kannywood.”
Ya ci gaba da cewa, “Abdulsalam Abdulkareem A.A. Zaura ɗan siyasa ne mai ƙauna da azamar taimakon kowane sashi na al’umma, musamman a Jihar Kano. Wannan ya sa ƙungiyar su ta ‘yan fim ta zama wata fitila a tafiyar siyasar gidan sa a wajen isar da saƙon jawo hankali ta hanyar nishaɗantarwa, faɗakarwa da tallace-tallace. Kuma sun yi zama da shi a Kano da Abuja sau da dama tare da tattauna abubuwan da za su kawo cigaba a masana’antar Kannywood, wanda hakan ya sa A.A. Zaura ya yi mana alƙawarin ba mu ’empowerment’ wanda kowa zai gamsu da cewa lallai an taimaka wa masana’antar.

“Hakan ya ba mu dama mu ka shirya jadawalin irin abubuwan da mu ke buƙata, wanda ya ƙunshi:
1. project funding
2. technical skills and training
3. marketing and distribution
4. production equipment.”
Ya ce da gani waɗannan abubuwan su na da buƙatar maƙudan kuɗaɗe da lokaci wajen samun damar aiwatar da su.
Ya ce hakan ya sa har zuwa yanzu su ke kan tattaunawa da A.A. Zaura da tsara yadda tallafin zai kasance ba tare da wani ƙorafi ba.
Shaban ya ce da zarar abubuwa sun saitu daga wajen A.A. Zaura, za a ga aiki da cikawa.
Shaban ya ce shi da Ahlan ba su da “wani tunani na cutar da kowa.”
Yanzu dai ƙwallo ta koma jikin ƙafar A.A. Zaura, ‘yan fim sun sa ido su ga wajen da zai buga ta.