HUKUMAR Tace Finafinai ta Jihar Kano da gidan talbijin na Arewa24 sun sasanta kan taƙaddamar da ta ɓarke tsakanin su game da wasannin kwaikwayo biyu na tashar, wato ‘Kwana Casa’in’ da ‘Gidan Badamasi’.
Yanzu hukumar ta amince a ci gaba da nuna wasannin guda biyu sakamakon yarda da Arewa24 su ka yi cewar za su cire duk wani sin wanda jama’a ke ƙorafi da shi, sannan kuma za su riƙa bada wasannin nasu ga hukumar domin ta tace su kafin a watsa su ga masu kallo.
A cikin wata sanarwa ga manema labarai da ya rattaba wa hannu, shugaban hukumar, Alh. Isma’il Na’abba (Afakallah), ya bayyana cewa wannan daidaito da aka samu ya biyo bayan zama da aka yi tsakanin hukumar tasa da jami’an gidan talbijin ɗin jiya Alhamis da yau Juma’a.
Ya ce ɓangarorin biyu sun amince za a cire sinasinan da ke ɗauke da abubuwan da al’umma ke ƙorafi a kan su waɗanda aka haska a shirin ‘Kwana Casa’in’ na makon jiya.
“Su Arewa24 sun amince za su cire guraren kafin ma a sake haska shirin, sannan sun amince da cewa kowanne fim ɗin Hausa da za su haska sai ya kasance wanda ya ke da shaidar tantancewa da ta fito daga Censorship Board,” inji Afakallah.
Mujallar Fim ta fahimci cewa ɓangarorin biyu sun yi zaman ne a hedikwatar Hukumar Tace Finafinan da ke Kano a ƙarƙashin Afakallah da wakilan Arewa24.
A wajen taron akwai sauran daraktocin hukumar.
Idan kun tuna, hukumar ta umarci gidan talbijin ɗin fa ya dakatar da nuna wasannin kwaikwayon guda biyu masu nisan zango har sai hukumar ta tace su.
Umarnin ya biyo bayan ƙorafin da wasu masu kallo su ka yi kan yadda aka nuno wasu matasa sun kama hannun mace a cikin shago da kuma cikin motar A Daidaita Sahu a shirin ‘Kwana Casa’in’ da aka haska ran Lahadi da ta gabata.
Umarnin hukumar ga tashar ya haifar da ce-ce-ku-ce a cikin jama’a, musamman ma dai a soshiyal midiya inda wasu su ka ce matakin hukumar ya yi daidai, yayin da wasu kuma su ka ƙalubalanci hurumin ta na ɗaukar wannan matakin.
A sanarwar da ya bayar a yau, Afakallah ya ce: “Yanzu dai a iya cewa an samu daidaito wanda hakan zai ba wa Arewa24 damar cigaba da haska shirye-shiryen wasan Hausa da su ke haskawa, amma fa sai an tace su daga Censorship Board.”
