Abin farin ciki kuma abin alfahari, a rayuwar Musulmi a wannan lokacin shi ne ya wayi gari cikin nasara ya ga yaran sa sun samu karatun da har suka kai ga sauke Alkur’ani mai girma.
Haka ne ya faru ga fitaccen Darakta a Kannywood, Hassan Giggs, da kuma matarsa, tsohuwar jaruma a Kannywood, Muhibbat Abdussalam.
A ranar Lahadi 3 ga Nuwamba 2024 ne aka yi taron bikin saukar karatun Alkur’ani mai girma na ‘yayansu biyu, wato Humaira Hassan Giggs da Azeema Hassan Giggs.

An yi taron saukar ne a bayan tashar Motar Mariri dake Ƙaramar Hukumar Kumbotso a cikin garin Kano. Kuma bayan an kammala taron, aka dawo gidan dake rukunin gidajen Danladi Nasidi inda aka ci gaba da shagalin biki, kuma ‘yan uwa da abokan arziƙi da dama sun halarci wajen domin taya su murna.

Cikin wani gajeran saƙo da ya saka a shafin sa na Facebook, Darakta Hassan Giggs ya ce:
“I am just full of excitement today alhamdulillah alhamdulillah’
“Ina alfahari da ku.
“Mostly credit goes to my beautiful wife @official_muhibbat_abdulsalam Allah miki albarka, ya sa ki gama da duniya lafiya.
“Humaira Hassan Giggs Azeema Hassan Giggs, wannan saukar da kuka yi Allah ya sa ku amfanar da al’ummar Musulmi ga baki ɗaya amin”.