• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Jarumi Ali Dawayya ya shirya taron buɗe sabon gidan abincin sa

by MUKHTAR YAKUBU
November 4, 2024
in Labarai
0
Jarumi Ali Dawayya ya shirya taron buɗe sabon gidan abincin sa

Daga hagu zuwa dama: Ali Dawayya, Ali Nuhu, da Ahmad Salisu Alkanawy, a lokacin buɗe gidan abincin.

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Fitaccen jarumi a Kannywood, Ali Dawayya, shi ma dai a yanzu ya raba ƙafa inda baya ga kasancewar sa jarumi kuma furodusa, a yanzu ya buɗe wani sabon gidan sayar da abinci na zamani mai suna Zabuja Restaurant.

A ranar Lahadi 3 ga Nuwamba 2024 ne aka yi taron bikin buɗe gidan abincin na Zabuja Restaurant dake Gidan Dan’asabe a kan titin gidan Zoo a Kano.

Taron buɗe gidan abincin wanda fitaccen Jarumi kuma M D na Hukumar Bunƙasa Fim ta Ƙasa, Ali Nuhu, tare da Ahmad Salisu Alkanawy suka jagoranta, ya samu halartar ‘yan fim da dama inda aka taru domin taya Jarumi Ali Dawayya buɗe sabon gidan sayar da abincin.

Ali Dawayya ya shaida wa mujallar fim manufar sa ta buɗe wajen sayar da abincin, inda yake cewa “A gaskiya na yi farin ciki da ganin jama’a masu yawa da suka halarci wannan taron na buɗe gidan abincin musamman Ali Nuhu da Ahmad Salisu Alkanawy da suka jagoranci buɗewar. Ina yi wa kowa fatan alheri.

“Wannan gidan sayar da abincin da na buɗe, na yi shi ne domin samar wa da kaina mafita, domin a yanzu harkar rayuwa ta wuce a tsaya ga sana’a ɗaya saboda yadda yanayi ya sauya.

Zabuja Restaurant

“To mu kuma a harkar mu ta fim sai ka ga mun tsaya ga ita kawai duk da ɗimbin buƙatu na rayuwa da suke ƙaruwa, don haka na ga baya ga kasancewa ta a matsayin Jarumi kuma furodusa, to ya zama wajibi na samar da wata hanyar dogaro saboda rayuwa kullum ta na sauyawa ne.

“Kuma a yanzu harkar abinci harka ce ta yau da kullum shi ya sa na zaɓi na buɗe wajen sayar da abincin kuma na samar da duk wani abinci na zamani don buƙatar masu saye, ko su zo su ci a nan ko su tafi da shi, ko kuma a je a kai musu a duk inda suke.

“Ina Godiya ga Allah, kuma ina godiya ga dukkan mutanen da suka halarci wannan taron na buɗe gidan sayar da abincin da na yi mai suna Zabuja Restaurant. Allah ya sa mun buɗe a sa’a.”

Loading

Previous Post

Gwamnati da kafafen yaɗa labarai abokan hulɗa ne, ba na adawa ba, inji Minista

Next Post

Humaira da Azeema, ‘yayan Darakta Hassan Giggs, sun yi saukar Alkur’ani

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Humaira da Azeema, ‘yayan Darakta Hassan Giggs, sun yi saukar Alkur’ani

Humaira da Azeema, 'yayan Darakta Hassan Giggs, sun yi saukar Alkur'ani

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!