• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 30, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Iyan-Tama na so Abba Gida-Gida ya yi wa ‘yan Kannywood da su ka yi tafiyar sa adalci

by DAGA ABBA MUHAMMAD
March 22, 2023
in Labarai
0
Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama

Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

TSOHON Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Arewa (AFMAN), Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama, ya yi kira da a yi adalci ga waɗanda su ka yi tafiyar siyasar Injiniya Abba Kabir Yusuf har ya samu damar lashe zaɓen zama gwamnan Jihar Kano.

Iyan-Tama ya bayyana haka ne a saƙon da ya tura wa mujallar Fim, kwana ɗaya bayan hirar musamman da ta yi da shi kan sakamakon zaɓen.

Iyan-Tama ya ce, “Ita siyasa dace ce; za ka ga wasu sun bauta mata amma ko kaɗan idan an ci zaɓe sai a manta da su. Waɗanda su ka ƙi tafiyar sai su shigo su yi babakere.”

Ya ci-gaba da cewa, “Ina tabbatar maka da cewa yanzu za ka fara ganin wasu daga cikin ‘yan fim ɗin da ba su yi tallar Abba ko kaɗan ba za su fito su ce su nasa ne ko kuma ai sun taimaka, bacin kuma ƙarya su ke yi. Allah ya sa Abba ya san su.”

Babban furodusan kuma shugaban kamfanin Iyan-Tama Multimedia, Kano, ya yi kira ga zaɓaɓɓen gwamnan da ya taimaka wa waɗanda su ka yi masa hidima ta basira da lokaci da shigo da jama’a don su zaɓe shi.

Ya kafa da misali Sunusi Oscar 442, Abba El-Mustapha, Maibulala, Tijjani Gandu, Abubakar Sani da sauran su, ya na faɗin: “Ai ba wanda zai ce bai san su ba a tafiyar Abba.”

Iyan-Tama ya ce: “Ina ba da shawara a yi duba,  a yi adalci. Kar a sake a yi abin da ake ce wa kura da shan bugu gardi da kwashe kuɗi.” 

Mujallar Fim ta ruwaito cewa yanzu haka tun kafin a je ko’ina har wasu ‘yan fim da su ka yi adawa da Abba Gida-Gida sun fara dawowa su na cewa su da ma can ‘yan Kwankwasiyya ne. 

Babban misali shi ne Mustapha Badamasi Naburaska, wanda a baya tafiyar Abba ya yi, amma ya koma tsagin su ɗan takarar jam’iyyar PDP, Dakta Yusuf Gawuna, har Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ba shi muƙamin mataimaki na musamman a ɓangaren farfaganda, amma yanzu ya dawo ɓangaren Abba bayan an lashe zaɓe. Akwai kuma Ali Artwork, Hudu Mazaje da wasun su waɗanda da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai za su yi ta dawowa.

Loading

Tags: Abba Gida-GidaAbba Kabir YusufAFMANbabakereGandujeGawunaHamisu Lamiɗo Iyan-TamaKannywoodKano
Previous Post

Mahaifin jarumar Kannywood Fati S.U. Garba ya kwanta dama

Next Post

Mukhtar SS ya zama baban Hafsa

Related Posts

Wani mai suna Bashir Abdullahi ya damfare ni miliyan bakwai da rabi, inji Halisa
Labarai

Wani mai suna Bashir Abdullahi ya damfare ni miliyan bakwai da rabi, inji Halisa

July 28, 2025
Gaskiyar magana kan ji-ta-ji-tar ‘mutuwar’ Aminu Ala
Labarai

Gaskiyar magana kan ji-ta-ji-tar ‘mutuwar’ Aminu Ala

July 28, 2025
KADIFF 2025: Uganda ta fi yawan finafinai a bikin baje-kolin na Kaduna – Israel Kashim Audu
Labarai

KADIFF 2025: Uganda ta fi yawan finafinai a bikin baje-kolin na Kaduna – Israel Kashim Audu

July 25, 2025
Karya dokar liƙi: Kotu ta ɗaure G-Fresh da Hamisu Breaker tsawon wata biyar-biyar
Labarai

Karya dokar liƙi: Kotu ta ɗaure G-Fresh da Hamisu Breaker tsawon wata biyar-biyar

July 24, 2025
‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar
Labarai

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar

July 23, 2025
Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Next Post
Jaririya Hafsa tare da baban ta, Malam Mukhtar

Mukhtar SS ya zama baban Hafsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!