JARUMAR Kannywood Maryam Aliyu Obaje, wadda aka fi sani da suna Madam Korede ko ‘Yar Fim, ta bayyana farin cikin ta game da gurbin karatu da ta samu a wata jami’a mai suna ‘ESGT University’ da ke Jamhuriyar Benin.
Bayan ta ɗora takardar ɗaukar ta a makarantar a Instagram, a ƙasa ta rubuta, “Babu lokacin ɓata lokaci”.
A zantawar da ta yi da mujallar Fim, jarumar, wadda ta ke zaune a Kaduna, ta ce: “Gaskiyar magana na yi matuƙar farin ciki sosai, domin abin ya yi min daɗi matuƙa.

“A da ina tunanin ba zan iya ba, sai ga shi Allah ya sa shi mai makarantar ya taho ya ba ni ‘scholarship’, zan tafi in je in yi karatu na. Kuma a yanzu kowa ya san cewa karatu ya fi komai muhimmanci a rayuwar nan. A gaskiya na yi matuƙar jin daɗi sosai.”
Allah ya ba da sa’a Madam Korede, ya kuma sa a fara lafiya, a ƙare lafiya.