FITACCEN jarumi Aminu A. Shariff (Momoh) ya ƙaryata labarin da ake yaɗawa cewa wai ya tsare wani mai kurar ruwa ya biya shi ɓarnar da ya yi masa a mota. Ya ce sam, ba a yi haka ba.
A ‘yan kwanakin nan labarai su ka yaɗu a soshiyal midiya ana cewa wai jarumin ya yi rigima da mai wani kurar ruwa.
A labarin, an ce wai shi Momoh ɗin ya buƙaci ɗan garuwan da ya biya shi kuɗin ɓarnar da ya yi masa.
Yayin da wasu sun soki jarumin da rashin adalci, wasu kuma sun yabe shi kan ya bi haƙƙin sa ne.
To amma da mujallar Fim ta waiwayi jarumin da maganar, sai ya kafa baki ya ce shi bai ma san daga wajen wa masu yaɗa labarin su ka samo labarin ba.
A cewar sa, kawai wasu ne su ke ganin sun mallaki waya kuma sun samu data ba su san amfanin ta ba, kawai su ke riƙa saka hotuna su na rubuta abin da suka ga dama.
Momoh, wanda kuma ɗan jarida ne, ya ce, “Ni ban samu wata matsala da mai kurar ruwa ba. Kawai dai abin da na sani wajen sati biyu da su ka wuce a Kantin Kwari wani mai mota a-kuri-kura, wadda aka fi sani da ƙurƙura, ya yi mini ɓarna a mota, kuma ganin bisa ganganci ya yi abin na nemi ya biya ni, kuma ya biya ni ɗin cikin maslaha, mu na wasa da dariya ni da su. Kuma ba wani abu da ya faru bayan wannan.
“Amma kawai bayan tsawon lokaci sai na ji an kira ni daga gidan wani rediyo, wai su na so su ji daga gare ni ga wani labari da wakilin su ya samo yanzu an ce mun yi rigima da mai kurar ruwa a kan ya yi mini ɓarna na ce sai an biya ni.
“To, sai na ce da su, ‘Amma shi wakilin naku ma bai san aikin sa ba in dai wannan shi ne labari da ɗumi-ɗumi. Idan ni ne ma dakatar da shi zan yi saboda labarin ya fi sati biyu, kuma shi sai yanzu ya kawo muku; kun ga ba aikin ya ke yi ba. Ya kamata a ce ya kawo tun a lokacin da abin ya faru’.”
A kan batun rashin dacewar da wasu ke cewa ya yi da ya nemi haƙƙin sa, Momoh ya ce: “Ni abin da na yi neman haƙƙi na yi na ɓarnar da aka yi mini a mota, kuma kowa ya na yin hakan idan ya so.
“Don haka ni abin da ya dace ne na yi. Ko da wasu su na ganin bai dace ba, to a wajen su ne hakan, amma ba a Musulunci ba, ba kuma a dokar ƙasa ba.
“Ni a matsayi na na wanda aka yi wa ɓarna, kuma wanda ya yi ya amince da hakan ya biya ni cikin sauƙi, to ka ga mun yi abin da ya dace.
“Don haka mutane bai kamata su mayar da abin wani abin magana daban ba. Amma saboda ba a san abin da zai zama labari ba, sai na ga ana ɗora hoto na da kurar ruwa ana ta yin labarai kala-kala, saboda an samu data a banza kuma ba a san amfanin da za a yi da ita ba.”
Jarumin ya yi kira ga masu yaɗa labarai a soshiyal midiya da su riƙa tantance labarin da za su riƙa sakawa ta hanyar bin diddigin labari kafin su saka shi don mutane su yarda da ingancin labarin nasu.
![]()







