JAGORAN shirya bikin bajekoli da gasar finafinai ta Afirka na Kano, wato ‘Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festival’ (KILAF), wanda ake shiryawa a duk shekara, Alhaji Abdulkareem Muhammad, ya bayyana cewa a bana sun fito da sabon tsarin taron wanda ya bambanta da na shekarun baya.
A yanzu haka dai shirye-shirye sun yi nisa wajen shirya babban taron, wanda shi ne karo na biyar da za a yi daga lokacin da aka fara shi.
A hirar sa da mujallar Fim, Alhaji Abdulkareem ya yi bayanin cewa: “Wannan taron da za a yi na bana ya zo da wasu tsare-tsare da su ka wuce na baya. Saboda a shekaru biyu da su ka wuce duk da matsalar korona ba mu samu yin taron ba, amma sai mu ka yi ta allon gani ga ka ta yanar gizo. To, a wannan ne za mu koma mu yi shi yadda mu ka saba a baya, sai dai kuma saboda cigaban da mu ka samu, za mu yi shi ta yanar gizo, sannan za mu yi taron da mu ka saba yi ido da ido.
“Sannan wani sabon abu da mu ka zo da shi, mun samar da wata kafa da za a yi wani gwaji na abubuwan da su ka shafi na al’ada kamar zane-zane da kuma abubuwan da ƙasashen Afirka su ke sarrafawa da kan su. Shi ma za mu yi baje-kolin sa wanda za mu ware masa rana guda a cikin shirin a ranaku biyar da mu ka ware na wannan bikin.”
Dangane da gasar finafinai kuwa, Alhaji Abdulkareem ya ce, “A wannan karon mun ware abubuwa guda goma sha shida waɗanda za a ci gasar su, sai kuma girmamawa ga mutane guda biyu waɗanda su ka bayar da gudunmawar su wajen bunƙasa finafinan Afirka.”
Bugu da ƙari, ya ce za a gudanar da taro inda za a gabatar da maƙalu.
Taken taron na wannan shekarar dai shi ne yadda ake gabatar da labaran fim a Afirka da kuma salon da za a inganta shi.
Abdulkareem ya ce: “Mun gayyaci masana da yawa da za su gabatar da takardu a wajen, kuma za a wallafa littafi da zai zama kundi ne na jigon da aka zaɓa.”

A game da rashin samun haɗin kan ‘yan fim na Kannywood a tarurrukan baya, cewa ya yi, “A wannan karon mun samu haɗin gwiwa da ƙungiyar MOPPAN don a shigo da su a yi harkar da su gaba ɗaya. Kuma mun inganta yadda za mu tallata abin yadda za mu samu shigowar finafinai daga sauran ƙasashen Afirka, yadda zai zama duk wasu masu yin fim da harsunan Afirka za su samu wakilci a cikin taron.
“Saboda haka ba wai Kannywood ne kawai za su yi ba, musamman a nan ƙasar za mu shigar da na Yarbawa, Ibo Nufawa da sauran harsunan Nijeriya da ake yi da kuma Swahili a wajen ɓangaren Afirka ta Gabas, har ma irin na Larabci daga irin su Tunusiya da Masar da Zamarmanci da ke Nijar.
“Kuma mu na sa ran yadda mu ka inganta harkar isar da saƙon taron, in-sha Allah za a samu shigowar su da wuri, ba tare da lokaci ya ƙure ba.
“Kuma tun farkon watan Agusta mu ka sanar da fara karɓar finafinan da za su shiga gasar.
“Da man mu na yin taron ne a watan Nuwamba na duk shekara, don haka lokacin ba canza ba. Don haka mun tsayar da ranakun 22 zuwa 27 ga Nuwamba ɗin, wanda zai zama ranar 26 shi ne za a yi gagarumin taron bayar da ‘awards’ ɗin.”
Babban furodusan ya yi kira ga ‘yan Kannywood da su fito kowa ya bayar da gudunmawar sa ta wajen da ya dace, “domin taron na kowa da kowa ne, in dai ya na kishin masana’antar finafinai ta Kannywood da kuma cigaban Afirka.”