• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, August 23, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

KILAF 2025: Za mu ci gaba da ƙarfafa wa matasa gwiwa don samar da finafinai masu nuna al’adun mu – Abdulkareem

* An karɓi finafinai 616 daga ƙasashe 717

by MUKHTAR YAKUBU
October 20, 2025
in Labarai
0
KILAF 2025: Za mu ci gaba da ƙarfafa wa matasa gwiwa don samar da finafinai masu nuna al’adun mu – Abdulkareem

Alhaji Abdulkareem Muhammad, Shugaban shirya KILAF

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

KWAMITIN shirya Bikin Baje-kolin Finafinai na Harsunan Afrika na Kano, wato Kano Indigenous Languages of Africa Film Market and Festival (KILAF Awards) na bana ya sha alwashin ci gaba da ƙarfafa wa matasan Nijeriya gwiwa wajen samar da finafinai na gargajiya da ke tallata ɗabi’u da al’adun nahiyar ta hanyar fasahar zamani.

Shugaban shirya bikin, Alhaji Abdulkareem Muhammad, shi ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai da aka gudanar a ofishin ƙungiyar ’yan jarida ta Nijeriya (NUJ) a Kano a jiya Lahadi don bayyana yunƙurin sa na tunkarar bikin na bana da za a yi shi a watan Nuwamba mai zuwa.

Alhaji Abdulkareem ya ce bikin KILAF ɗin, wanda shi ne karo na takwas, ya karɓi finafinai 616 daga ƙasashe 717, yayin da ƙasashe 12 za su shiga sahun masu karɓar baƙunci.

Ya ƙara da cewa a yayin shirin taron, an buga mujallu guda shida da za su taimaka ga masana harkar finafinai da jami’o’i wajen koyar da sana’ar.

“Akwai ƙasashe 14 da ke fafatawa domin lashe kyaututtuka, wasu daga cikin finafinan ma haɗin gwiwa ne da ƙasashen Birtaniya, Amurka, Isra’ila da Italiya,” inji shi.

Ya ce za a zaɓi masu nasara daga jerin finafinai da aka gabatar ta hannun alƙalai bakwai, kuma za a bayyana sakamakon a ranar 8 ga Nuwamba, 2025.

Ya ci gaba da cewa: “Akwai rukunai 18 na kyaututtuka da za su fito daga cikin nominations 87, kuma kowanne ɗan takara ya cancanci yabo saboda ƙwarewar da ya nuna.

“Don haka KILAF na taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa ilimi da nazari a fannin shirya finafinai, kuma muna alfahari da bayar da gudunmawa a wannan fage.”

Shugaban ya bada sanarwar cewa za a gudanar da taron ƙarfafa wa mata 100 masu shiga harkar kafafen yaɗa labarai gwiwa a karo na biyu a wani sabon ɓangare da aka ƙara a bara wanda zai gudana a Makarantar Kasuwanci ta Ɗangote (Dangote Business School) da ke Jami’ar Bayero, Kano, a ranar 8 ga Nuwamba daga ƙarfe 10 na safe zuwa 2 na rana.

A cewar sa, an tsara shirin ne domin ƙarfafa shiga da nasarar mata a harkar kasuwancin kafafen yaɗa labarai.

Ya ce: “Za mu gayyato mahalarta daga kafafen yaɗa labarai, ƙungiyar mata ’yan jarida (NAWOJ), ƙungiyar mata (NCWS), da ƙarfafa ƙungiyoyin kare haƙƙin mata.

“KILAF tana fatan ganin sabbin haziƙan matasa da mata suna amfani da finafinai wajen kare martabar harshen gida da al’adun Afrika.”

Loading

Tags: Abdulkareem Muhammadal'adun gargajiyabikin baje-koliKanoKILAF 2025matamatasa
Previous Post

Za a rufe rajistar taron ranar Marubutan Hausa ta Duniya ranar Alhamis

Next Post

Furodusa a Kannywood, Abdul Amart ya biya wa jaruma Halisa Muhammad kuɗin tafiya neman magani

Related Posts

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Tsohuwar matar Adam Zango, Maimuna Musa, ta tabbatar da dalilin rabuwar auren su
Labarai

Tsohuwar matar Adam Zango, Maimuna Musa, ta tabbatar da dalilin rabuwar auren su

August 2, 2026
Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama
Labarai

Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama

August 2, 2026
Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11
Labarai

Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11

August 1, 2026
Next Post
Furodusa a Kannywood, Abdul Amart ya biya wa jaruma Halisa Muhammad kuɗin tafiya neman magani

Furodusa a Kannywood, Abdul Amart ya biya wa jaruma Halisa Muhammad kuɗin tafiya neman magani

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!