A YAU Alhamis ne za a buɗe Bikin Baje-kolin Finafinai na Harsunan Afrika na Kano, wato Kano Indigenous Languages Africa Film Market and Festival (KILAF).
Taron, wanda za a yi shi a Kano, zai shafe tsawon kwanaki uku, daga ranar Alhamis zuwa Asabar, 6-7 ga Nuwamba, 2025.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa a taron za a gudanar da muhimman abubuwa da suka haɗa da jawabai, da kalankuwa, baje-kolin kayayyakin gargajiya na Afrika kamar abinci, tufafi, da zane-zane da sassaƙe-sassaƙe na Afrika, da kuma bayar da kyaututtuka ga finafinan da suka yi nasara a gasar.
Takardar jadawalin taron da kwamitin tsara taron ya fitar ta nuna cewa za a yi taron ne daga ƙarfe 9 na safe zuwa ƙarfe 9 na dare a sabon mazaunin Jami’ar Bayero, Kano.
Za a fara da maraba da baƙi, da tantance finafinan da suka shiga gasar, da gabatar da abincin gargajiya na Afrika wanda aka saka masa suna African Kitchen.
Gobe Juma’a za a fita yawon buɗe ido da misalin ƙarfe 9 na safe, inda za a zagaya da baƙi mahalarta taron cikin Kano domin nuna masu tsarin al’adun garin da masarauta da sauran abubuwan tarihi da al’adu, sannan akwai cin abinci na musamman da Ƙungiyar Dattawan Arewa (ACF) takan shirya wa halarta taron, da ma sauran abubuwa da dama.
A rana ta ƙarshe za a yi bita kan fim da kuma jawabi a kan maudu’in “Mata da Aikin Jarida”.
A wannan ranar har ila yau za bayyana sunayen jarumai da finafinan da suka yi nasara a gasar, wato Awards Night, wanda za a yi a ɗakin taro na otal ɗin Bristol.
Tuni dai manyan baƙi suka fara isowa Kano daga sassa daban-daban na duniya da suka haɗa da nahiyoyin Afrika, Turai da Asiya.
![]()







