ƘUNGIYAR Kare Haƙƙin Masu Harkar Fim (AVRS) ta yi kira ga shugabannin harkar fim na Kannywood da su mayar da hankali wajen ɗaukar batun kiwon lafiyar membobin su da muhimmanci.
Kiran yana cikin saƙon ta’aziyyar rasuwar Alhaji Mato Yakubu, wanda aka fi sani da Malam Nata’ala, wanda Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai na ƙungiyar, Alhaji Makama Sani Mu’azu, ya rattaba wa hannu a yau.
Jarumin ya rasu a Asibitin Jami’ar Maiduguri (UNIMAIDTH) bayan ya yi fama da ciwon daji.
Cikin alhini, AVRS ta ce: “Mun yi murnar cewa mun bada gudunmawar kuɗi gare shi a lokacin da yake sa buƙatar su.
“Muna miƙa saƙon ta’aziyyar mu ita ma ga masana’antar fim ta Nijeriya, kuma muna fatan wannan abu zai zama izna ga masana’antar domin ta ɗauki kiwon lafiyar haziƙan jaruman mu da muhimmanci.
“Muna addu’ar Allah ya agaji iyalan Malam Nata’ala a wannan mawuyacin lokacin, amin.”
Idan kun tuna, a ranar 3 ga Satumba na wannan shekarar mujallar Fim ta bada labarin yadda AVRS ta ba Malam Nata’ala tallafin kuɗi N250,000 a kan rashin lafiyar sa.
Ƙungiyar ta miƙa tallafin ne ta hannun Makama Sani Mu’azu, wanda tsohon shugaban MOPPAN ne kuma dattijo a Kannywood.
![]()







