• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

KILAF Awards 2025: Za a buɗe bikin baje-koli da fidda zakarun finafinan Afrika a yau a Kano

by MUKHTAR YAKUBU
November 6, 2025
in Labarai
0
KILAF Awards 2025: Za a buɗe bikin baje-koli da fidda zakarun finafinan Afrika a yau a Kano
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

 

A YAU Alhamis ne za a buɗe Bikin Baje-kolin Finafinai na Harsunan Afrika na Kano, wato Kano Indigenous Languages Africa Film Market and Festival (KILAF).

Taron, wanda za a yi shi a Kano, zai shafe tsawon kwanaki uku, daga ranar Alhamis zuwa Asabar, 6-7 ga Nuwamba, 2025.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa a taron za a gudanar da muhimman abubuwa da suka haɗa da jawabai, da kalankuwa, baje-kolin kayayyakin gargajiya na Afrika kamar abinci, tufafi, da zane-zane da sassaƙe-sassaƙe na Afrika, da kuma bayar da kyaututtuka ga finafinan da suka yi nasara a gasar.

Takardar jadawalin taron da kwamitin tsara taron ya fitar ta nuna cewa za a yi taron ne daga ƙarfe 9 na safe zuwa ƙarfe 9 na dare a sabon mazaunin Jami’ar Bayero, Kano.

Za a fara da maraba da baƙi, da tantance finafinan da suka shiga gasar, da gabatar da abincin gargajiya na Afrika wanda aka saka masa suna African Kitchen.

Gobe Juma’a za a fita yawon buɗe ido da misalin ƙarfe 9 na safe, inda za a zagaya da baƙi mahalarta taron cikin Kano domin nuna masu tsarin al’adun garin da masarauta da sauran abubuwan tarihi da al’adu, sannan akwai cin abinci na musamman da Ƙungiyar Dattawan Arewa (ACF) takan shirya wa halarta taron, da ma sauran abubuwa da dama.

A rana ta ƙarshe za a yi bita kan fim da kuma jawabi a kan maudu’in “Mata da Aikin Jarida”.

A wannan ranar har ila yau za bayyana sunayen jarumai da finafinan da suka yi nasara a gasar, wato Awards Night, wanda za a yi  a ɗakin taro na otal ɗin Bristol.

Tuni dai manyan baƙi suka fara isowa Kano daga sassa daban-daban na duniya da suka haɗa da nahiyoyin Afrika, Turai da Asiya.

Loading

Tags: finafinan Afrikaharsunan AfrikaKanoKILAF 2025
Previous Post

Rasuwar Malam Nata’ala: AVRS na so a ɗauki batun kiwon lafiyar jaruman Kannywood da muhimmanci

Next Post

Furodusa Sani Sule Katsina zai aurar da ‘yar sa Ramlat ran Juma’a

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Furodusa Sani Sule Katsina zai aurar da ‘yar sa Ramlat ran Juma’a

Furodusa Sani Sule Katsina zai aurar da 'yar sa Ramlat ran Juma'a

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!