• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Lamaj ta ƙaryata Sha’ani kan rashin kuɗi a asusun MOPPAN ta Kaduna

by DAGA ABBA MUHAMMAD
September 20, 2022
in Labarai
0
Hajiya Fatima Ibrahim (Lamaj)

Hajiya Fatima Ibrahim (Lamaj)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

TSOHUWAR Shugabar Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafina ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kaduna, Hajiya Fatima Ibrahim Ahmad (Lamaj) ta ƙaryata maganar da mataimakin shugaban ƙungiyar ya yi na cewa wai ba ta bar masu ko sisi a asusu ba.

Ta ce ai ita ce ma ta ke bin su kuɗaɗe.

Idan kun tuna, a makon jiya mujallar Fim ta ruwaito sabon Mataimakin Shugaban ƙungiyar, Malam Suleiman Sha’ani, ya na faɗin cewa Lamaj ba ta bar ko kwabo a asusun ƙungiyar ba a ƙarshen mulkin ta.

Lamaj ta na jawabi a wajen taron MOPPAN ta Kaduna

A martanin da ta yi wa masa a yayin zantawar ta da mujallar Fim, Lamaj ta ce: “Alhamdu lillahi, na ji maganar da mataimakin shugaban MOPPAN ya yi. Na gode wa Allah, shi shugaban ƙungiyar na yanzu shi ne sakatare na a lokacin mulki na, shi ma kuma ya san MOPPAN ba ta taɓa samun naira ɗaya ba. 

“Ni da na ke tsohuwar shugabar MOPPAN, hatta ‘letterheads’ ni na ranci kuɗi na yi; haka rantsar da mu da aka yi, ni na ranci kuɗi aka rantsar da mu. 

“Sannan ‘forms’ da aka buga na MOPPAN, ni na ranci kuɗi na ba da aka buga. Yanzu ni ke bin MOPPAN kuɗi.

“Haka kuma shi kan shi mataimakin shugaban da ya ke magana, na ba shi ‘forms’ hamsin na ‘yan wasa, har yau bai yi ‘remitting’ ko naira ba ya ce waɗannan sun sayi ‘forms’ ba. 

“Sannan akwai ‘forms’ da aka saya ta hannu na, na kira shi ofis na na ba shi kuɗi. In kuma ya ce ƙarya ne, ya fito ya kare kan shi.”

Lamaj ta ci gaba da cewa, “Dukkan ciyamomin ‘guilds’ babu wanda ban kira na ba shi fom guda hamsin a kan ya saida wa membobin shi ba saboda su yi ‘remitting’ kuɗi ga MOPPAN. Wasu sun saida, wasu ba su saida ba; in fact, babu wanda ya kira ni ya sanar da ni abin da ke faruwa da ‘forms’ ɗin. 

“Kuma duk wanda ya musa, a kira ni ga ni ga su mu yi magana. 

“Kuma shi mataimakin shugaba da ya ke cewa MOPPAN na baya ba ta bar komai ba, nawa ya ba ni na ‘forms’ ɗin da na ba shi? Waɗanda na saida na hannu na na ba shi kuɗin. Ka faɗa wa kowa, ni na faɗa maka na ba shi kuɗi.

“Sannan ciyaman na ‘cinematography’ shi ma bai ba ni ko sisi ba na ‘forms’; in fact, waɗanda na saida a ofis ɗi na, na kira shi ya zo ofis ɗi na na ba shi kuɗin.”

Lamaj ta ce, “Allah ya jiƙan Sani Ciyaman! Shi ma mutanen da su ka zo sayen ‘form’ a kan za su yi rijista na mawaƙa, na kan ce su neme shi ko Baban Kausar su sayi fom a wurin su. Kuma in aka je wurin Baban Kausar, sai ya tura su wurin marigayi Sani Ciyaman, na san sun saida ‘forms’, naira ba a kawo min ba har na sauka a kujerar MOPPAN.

“Yanzu ni ke bin MOPPAN kuɗi. Kuma shi Ɗanmaliki, wato P.R.O. na MOPPAN, shi ne shaida na a kan wannan magana da na faɗa maka.”

Loading

Previous Post

Kotu ta hana beli ga matasan da ake zargi da yin zamba da ɓatanci da sunan Iman Sani Danja

Next Post

Furodusa Usman Mu’azu ya yi addu’ar alheri a bikin Amira ɗiyar aminin sa, marigayi Isyaku Forest

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Amarya Aisha Isyaku Forest (Amira) tare da aminin mahaifin ta, Alhaji Usman Mu'azu, wanda ya tallafa wajen bikin ta da Habeeb

Furodusa Usman Mu'azu ya yi addu'ar alheri a bikin Amira ɗiyar aminin sa, marigayi Isyaku Forest

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!