MAHAIFIN tsohuwar jaruma Safiya Musa ya kwanta dama.
Alhaji Musa Makka, mai kimanin shekaru 98 a duniya, ya rasu a yau Talata, 22 ga Disamba, 2020 da misalin ƙarfe 1:00 na rana, a Asibitin Sojoji da ke cikin barikin 1 Division a Kawo, Kaduna.
Kafin rasuwar sa, ya sha fama da gyambon ciki (ulcer), wanda ashe ciwon ajali ne.
Marigayin ya yi jinyar kwanaki huɗu a asibitin, daga bisani aka dawo da shi gida, kuma aka maida shi a jiya Litinin, yau kuma Allah ya ɗauki ran sa.
Alhaji Musa ya rasu ya bar mata biyu, ‘ya’ya 34, jikoki 180, da tattaɓa kunne 50. Daga cikin ‘ya’yan nasa akwai ita fitacciyar jarumar finafinan Hausa, wato Hajiya Safiya Musa, wadda ke aure a Zariya yanzu.
Allah ya jiƙan sa da rahama, ya kuma albarkaci dukkan abin da ya bari, amin.