FITACCEN mawaƙin siyasa kuma shugaban ƙungiyar mawaƙa ta 13×13, Alhaji Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara), ya shirya wani taron addu’a na musamman domin yi wa ƙasa addu’a dangane da halin da ake ciki na rashin tsaro.
A safiyar yau Litinin aka gudanar da addu’ar a ɗakin taron da ke Titin Murtala Muhammed a Kano.

An shafe kusan wuni guda ana yin addu’o’i da karatun Alƙur’ani kan zaman lafiya da tsaro, saboda halin da Nijeriya ta ke ciki, da kuma neman kawo mafita musamman a game da zaɓen 2023 da ya ke tunkarowa.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa a taron, masu jawabi sun yi nasihohi kan yadda ya kamata a kyautata ɗabi’u da kuma haƙurin zama tare, sannan sun ja kunnen mahalarta taron da su riƙa kyautata mu’amalar su da juna a wannan lokacin da kuma yi wa juna fatan alheri domin ta haka ne za a samu a fita daga cikin halin da aka shiga.

A wani ɓangare kuma taron ya zama wani dandali na sada zumunta a tsakanin masu harkar fim da mawaƙa domin kuwa dukkan ɓangarorin ‘yan fim da mawaƙan Kannywood sun halarci wajen.
An dai yi addu’o’i tare da saukar Alƙur’ani. Bayan an kammala kuma aka yanka raƙumi guda biyu, aka raba sadaka.

