• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Abin da ya sa na shirya taron addu’a ga ƙasa – Rarara

by DAGA ABBA MUHAMMAD
August 1, 2022
in Labarai
0
Dauda Rarara ya na jawabi kan dalilin taron addu'ar

Dauda Rarara ya na jawabi kan dalilin taron addu'ar

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCEN mawaƙin siyasa, kuma shugaban ƙungiyar 13X13, Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara), ya bayyana dalilin sa na shirya taron saukar Alƙur’ani da yi wa ƙasa addu’a domin matsalar tsaro da ta ke fama da ita.

A yayin da ya ke yi wa manema labarai ƙarin bayani game da taron, Rarara ya ce, “Wannan taro da ke magana, ni shugaba ne na ƙungiyar 13X13, ma’ana President, amma taron in aka duba za a ga ba ‘yan 13X13 aka ce ba, mun ce mu kira mutane ne waɗanda su ke faɗakarwa, ma’ana ‘yan fim da kuma alarammomi ‘yan’uwa na mu zo mu karanta Alƙur’ani a kan waɗannan abubuwa da su ke faruwa a ƙasa, musamman arewacin ƙasar nan.  

“To, a gaskiya mu na neman addu’o’in mutane, kuma dama aikin 13X13 ta nuna wa mutane  abin da ya kamata su riƙa yi. 

“Abin da ya sa mu ka shirya wannan taro, saboda mu na buƙatar addu’a, aikin finafinai da aikin waƙoƙi babu abin da ya kai su son zaman lafiya, saboda idan babu zaman lafiya abin ba yiwuwa zai yi  ba, duk abin da ake tsammani ba zai yiwu ba. 

“Don haka zaman lafiyar mu ke so, musamman zaman lafiya a cikin mu, zaman lafiya a ƙasar mu, musamman zaman lafiya a masana’antar mu. 

“Saboda abubuwa su na ta faruwa, wanda ko da ko babu, to da mu a ciki. Domin wani ke ɗaukar abin ya yaɗa, wanda bai sani ba in ya gani abin ya ɗaga masa hankali. Kuma ba su na yi ba ne don a gani a yi addu’a, sai don su ɗaga wa mutane hankali. 

Alarammomi su na saukar Alƙur’ani

“Kuma wannan abu duk duniya ake yi, amma mu ƙasar mu mu ke gani ko garin, ko gidan mu. To, ta nan ya kamata mu fara duba ta ina ne za mu fara gyara wannan abu tukuna, sai na ga lallai sai gyaran ya fara daga cikin mu, shi ya sa na shirya wannan taro. 

“Kuma da ma abin da ya kamata mu yi kenan, gida-gida, masallatai-masallatai, coci-coci da duk wani wuri da ya kamata a roƙi Ubangiji don ya kawo mana ƙarshen wannan abu. Shi ya kamata mu zauna mu yi.”

Shin ko Rarara ba ya tunanin mutane za su ce kura ya rufo da fatar akuya, kawai ya shirya wannan taro ne saboda ɗan takarar sa Bola Tinubu? 

Sai ya amsa da cewa, “A’a, mu ai yanzu maganar ƙasa mu ke yi, ba maganar ɗan takara mu ke yi ba. In aka ce maganar ƙasa, ana maganar abin da zai raya ƙasar ne baki ɗaya, sai wannan ƙasar ta gyaru sannan Bola Tinubu zai ce ya na takara ko wanin sa ya ce ya na takara.

“Saboda haka, mu yanzu duk mai tallar Bola Tinubu kamata ya yi a ce ya yi addu’a, zaman ƙasar nan lafiya shi ne zai taimaki duk siyasar da za a yi. Don haka babu maganar Bola Tinubu ko wani a gefe ba. Wani ma zai ce shugaban ƙasa, duk ba wannan ba ne. 

“Mu idan shugaban ƙasa zai yi nashi, jami’an tsaro su yi nasu, to mu ma akwai rawar da za mu taka. Maigida ma wanda ya ke shi da matan sa akwai rawar zai taka, tunda kai ka ce mulkar ka ake yi, amma ba ka yarda ana mulkar ka ba. Don yanzu in an ce ka kwana bakwai ba ka fita ba, cewa za ka yi babu wanda ya isa. 

“Ya kamata mu gane wannan abu duka sai mun haɗu, mu taimaki jami’an tsaro da ‘information’, mu taimaki kan mu in jami’an tsaro su ka ce mana mu yi kaza mu yi, lallai wannan abu za mu taru mu kai ƙarshen waɗannan abubuwan. 

“Amma duk abin da za mu yi, wani zai ce ne mun yi don wane. Mu Alƙur’ani ne mu ka ce a karanta a yi addu’a, ba ji aka yi mun saka kiɗa ana cewa ‘Jagaba Shi Ne Gaba’ ba. Mun ce a karanta Ƙur’ani, don ƙasar mu ta samu zaman lafiya. 

“Kuma duk wanda aka gani a nan, mutane ne da su ke ɗaukar abu su na ɗorawa a kafafen sada zumunta miliyoyin masoyan su su na gani, kuma su na koyi da su. To yau mun ce a karanta Alƙur’ani, babu wani abu da babu maganin sa a ciki, shi ya sa mu ka taru a nan.

“Kuma musamman mu ka kira dattijai mutanen mu na cikin masana’antar nan mu ka ce su zo za mu faɗakar da mutane a kan abin da ya fi dacewa, a yanzu abin da Nijeriya ke buƙata shi ne mu riƙe addu’a.”

Dauda Rarara ya na jawabi kan maƙasudin taron

Wannan taro dai sama da alarammomi 200 ne su ka yi karatun, a cikin su har da shi kan shi Daudan. Kuma sauka goma sha tara aka yi. 

Bayan an idar da saukar Alƙur’anin ne kuma sai aka shiga yin addu’o’i.

An yanka raƙuma har biyu domin yin sadaka, kamar yadda mujallar Fim ta ruwaito a labarin taron na farko. 

Haka kuma an raba kuɗi ga dukkan waɗanɗa su ka halarci taron.

A ƙarshen taron, Rarara ya na raba kuɗin mota ga mahalarta
Lokacin da Malam Inuwa Muhammad ya yanka raƙumi

Loading

Tags: alarammomiAlƙur'ani.Bola TinubuDauda Kahutu RararaKannywoodKanoTaroZaɓen 2023
Previous Post

Matsalar tsaro: Rarara ya shirya taron yi wa ƙasa addu’a

Next Post

Harkar fim a yanzu mun yi girman da za mu bar wa yara – Lilisco

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Idris Shu'aibu Lilisco: An manyanta

Harkar fim a yanzu mun yi girman da za mu bar wa yara - Lilisco

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!