• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Matsaya a Kano: Daga yanzu Hisbah ba za ta ƙara tunkarar ‘yan fim ba

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
November 21, 2023
in Labarai
0
Sheikh Daurawa (a hagu) da El-Mustapha a lokacin taron

Sheikh Daurawa (a hagu) da El-Mustapha a lokacin taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
DAGA yanzu, Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ba za ta ƙara tunkarar ‘yan fim kai-tsaye kan wani abu da ya taso game da ‘yan fim ba a aikin ta, sai dai ta waiwayi Hukumar Tace Finafinai saboda ita ce hukuma mai kula da ‘yan fim, Allah-basshi ita ta san matakin da za ta ɗauka.
Wannan ya na daga cikin matsayar da aka cimma a wani zama na musamman da hukumomin biyu tare da jagororin Kannywood su ka yi jiya a Kano.
Zaman ya biyo bayan tayar da jijiyar wuya da aka yi a makon jiya tsakanin wasu ‘yan fim da Hukumar Hisbah a sakamakon kiran da ta yi masu wanda su ka ƙaurace mata.
Idan kun tuna, jarumi Abdallah Amdaz ya yi wani jawabi a gaban shugabannin hukumar wanda wasu ‘yan Kannywood su ka ce tozarci ne ga masana’antar, kuma shi ba shugaba ba ne a harkar fim da har zai wakilci ‘yan fim a zama da hukuma.
A jiya dai ainihin shugabannin Kannywood na haƙiƙa sun yi zama da hukumar a ofishin Hisbah ɗin inda aka ƙulla yarjejeniyar yin aiki tare domin kawo gyara kan abubuwan da ake ganin su na haifar da matsala a cikin al’umma.
A taron, akwai Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, da Shugaban Hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Ƙungiyar Ƙwararru Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) tare da ta Dattawan Kannywood su ne su ka wakilci ‘yan fim a zaman, don haka ya kasance ɗaiɗaiku ne su ka je, ba zuwan baki ɗayan ‘yan fim ba ne.
Jami’an Hisbah da na Hukumar Tace Finafinai da shugabannin Kannywood
A lokacin da aka fara taron an buƙaci ‘yan jarida irin su mujallar Fim da su fita har sai bayan an kammala tattauwar za a neme su.
A zaman, shugaban MOPPAN na ƙasa, Dakta Ahmad Sarari, ya yi bayani a kan wacece Kannywood, kuma su wanene ‘yan Kannywood.
Ɗaya daga cikin dattawan Kannywood kuma, Malam Khalid Musa, shi kuma ya yi nasa jawabin mai taken “Tsakanin Malamai Da Kuma ‘Yan Kannywood.”
Shi ma Alhaji Abba El-Mustapha ya yi jawabi a kan matsayin hukumar sa da matakin da ta ke ɗauka kan abubuwan da ke faruwa a Kannywood don ganin an gyara tarbiyya.
Sai dai a taron ba a shirya za a yi tambaya ko sharhi ba don ba a tsawaita jawabi ba.
An samar da matsaya a kan cewa za a samar da wani tsari na fahimtar juna tsakanin Hisbah da Kannywood, sannan za a shirya taro aƙalla na kwana uku nan gaba tsakanin hukumar da malamai da Hukumar Tace Finafinai da kuma ‘yan Kannywood don a fahimci juna.
A nan ne kuma aka tsaida maganar cewa daga yanzu duk wani abu da ya taso na aikin Hisbah, ba za ta tunkari ‘yan fim ba, sai dai ta koma ga Hukumar Tace Finafinai domin ita ce hukumar da gwamnati ta kafa don kula da ‘yan fim, ita kuma ta san matakin da za ta ɗauka.
Bugu da ƙari, shugabannin Kannywood ɗin sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta samar da makarantar shirya finafinai don koyar da harkar fim.
Daga dama: Dakta Sarari, El-Mustapha, da Ado Ahmad Gidan Dabino. Daurawa ne a teburin sa
Wani sashe na jagororin Kannywood a taron

 

Loading

Previous Post

KILAF 2023: An yi liyafar maraba da baƙi

Next Post

KILAF 2023 rana ta 3: An yi jawabai da bada darussa kan harkar fim

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
KILAF 2023 rana ta 3: An yi jawabai da bada darussa kan harkar fim

KILAF 2023 rana ta 3: An yi jawabai da bada darussa kan harkar fim

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!