• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Mawaƙi Sufin Zamani ya ba ‘yan fim haƙuri, ya wanke su da baiti biyu

by DAGA ALI KANO
June 24, 2022
in Labarai
0
Sarfilu Umar Zarewa (Sufin Zamani) a cikin bidiyon ban-haƙuri da ya saki a yau

Sarfilu Umar Zarewa (Sufin Zamani) a cikin bidiyon ban-haƙuri da ya saki a yau

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MAWAƘIN nan wanda ya ɓata mata ‘yan fim a wata waƙa, Malam Sarfilu Umar Zarewa (Sufin Zamani), ya bayyana nadamar abin da ya yi tare da ba su haƙuri, kwana ɗaya bayan ya samu beli daga Hukumar Tsaron Ƙasa (DSS).

Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba ku labarin yadda hukumar ta tsare shi daga shekaranjiya zuwa jiya sakamakon ƙarar sa da Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta kai mata.

A daren yau Sufin Zamani ya saki bidiyon da ya yi inda ya ba ɗaukacin ‘yan fim haƙuri kan waƙar tozarcin da ya yi wa mata ‘yan fim, waɗanda ya ce wai ba su son zaman aure.

Kakakin MOPPAN, Malam Al-Amin Ciroma, ya ce bayar da haƙurin da Sufin Zamani ya yi ya na daga cikin sharuɗɗan da DSS ta gindaya masa. 

A bidiyon, mawaƙin ya ce, “Yau aƙalla shekara goma sha huɗu kenan da fara sana’a ta ta waƙa, sannan aƙalla na yi waƙa ta kai guda ɗari da saba’in da huɗu.

“Cikin ikon Allah, duk waƙoƙin da na ke yi ban taɓa yin wata waƙa da na zagi wani ko na ci zarafin wani ko na baƙanta wa wani ba. Kullum buri na shi ne na faranta wa mutane, ba na baƙanta wa mutane ba, shi ya sa waƙoƙi na gaba ɗaya ma ɓangaren barkwanci ne.

“To amma an samu akasi a wannan lokaci, ‘yan kwana kwanan bayan nan sai ga shi na yi wata waƙa wacce gaba ɗaya ba ta yi wa ɗaukacin ilahirin ‘yan masana’antar finafinan Hausa daɗi ba.

“To, zan yi amfani da wannan dama in roƙi afuwar ku, don Allah don Annabi ku yafe min.

“Jaruman masana’antar Kannywood, mazan ku da matan ku, an shaide ku da kun yi shura wajen ƙaunar ku ga Annabi Muhammadu. To, ku yi haƙuri don Annabi Muhammadu. Na san  Bahaushe ya ce ‘matar na tuba ba ta rasa miji’, to ina da tabbacin shi ma ‘mijin na tuba’ ba zai rasa mata ba.

“Kamar yadda na yi waccan waƙa ba ta yi maku daɗi ba, in-sha Allahu zan yi wata kuma wacce za ta faranta maku, za tai maku daɗi.”

Daga nan sai ya rera baiti biyu na waƙa kamar haka:

“‘Yan wasan Hausa mun shaida ku na riƙe aure,Mata da mazan ku mun gane ku na riƙe auren sunna.

‘Yan wasan Hausa mun gane ku na riƙe aure,Mata da mazan ku ba kwa wasa fa da auren sunna.”

Sufin Zamani dai ya samu beli ne a jiya Alhamis, 23 ga Yuni, 2023 bisa waɗannan sharuɗɗan:

1. Zai yi bidiyo da odiyo na ban-haƙuri da kuma ƙaryata kan sa game da waƙar ɓatancin da ya yi.

2. Zai yi waƙa kishiyar wacce ya yi, wato ya yabi matan Kannywood, ya faɗi alherin su kuma ya nuna masu zaman aure ne.

3. Zai rubuta wa MOPPAN takardar ban-haƙuri.

4. Zai yi wa hukumar alƙawari a rubuce, wato ‘undertaking’, cewar ba zai ƙara yin ɓatanci ga duk wani ɗan fim ba.

5. Bayan ya yi wannan kuma hukumar DSS za ta yi masa hukuncin  da ya dace, domin ya yi musu ƙarya a farkon kamun da aka yi masa.

MOPPAN ta ce yarjejeniyar ta biyo bayan amincewar da ya yi cewa ya aikata laifin.

Loading

Tags: Al-Amin CiromaaureɓatanciDirectorate of State SecurityDSShausa filmsmatan KannywoodMOPPANSarfilu Umar ZarewaSufin Zamani
Previous Post

Dalilin da ya sa INEC ta karɓi sunan Sanata Lawan wanda bai shiga takara ba, maimakon na Machina wanda ya lashe zaɓe – Kwamishinan Zaɓe

Next Post

Hukumar DSS ta tsare mawaƙi Sufin Zamani kan cin zarafin matan Kannywood

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Malam Sarfilu Umar Zarewa (Sufin Zamani)

Hukumar DSS ta tsare mawaƙi Sufin Zamani kan cin zarafin matan Kannywood

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!