ƘUNGIYAR Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta miƙa saƙon ta’aziyyar rasuwar hamshaƙin ɗan kasuwa Alhaji Aminu Ɗantata ga Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da al’ummar jihar.
Ƙungiyar ta yi saƙon ne ta wasiƙa wadda shugaban ta na riƙo, Alhaji Shehu Hassan Kano, ya rattaba wa sannu.
Ƙungiyar ta ce, “Cikin tsananin baƙin ciki da tsananin rashi muka samu labarin rasuwar hamshaƙin ɗan kasuwa kuma fitaccen ɗan Kano, Alhaji Aminu Ɗantata.
“Alhaji Ɗantata ba wai kawai wani babban jigo ne a harkar kasuwanci a Jihar Kano da Afrika ta Yamma ba, har ma ya kasance mai kishin al’umma, mai taimakon jama’a, kuma abin koyi.
“Jagorancin sa na hangen nesa, basirar kasuwanci, da zuba jari a ɓangarori daban-daban sun taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki, samar da damarmaki marasa adadi da kuma ɗaukaka al’umma da suka wuce iyakokin Kano.
“Gudunmawar da ya bayar a fannin kasuwanci da masana’antu sun bar tarihi a cigaban yankin.
“Rasuwar sa babban rashi ne ba ga dangin sa da ’yan kasuwa kaɗai ba, har ma ga ɗaukacin Jihar Kano da ma yammacin Afirka.
“Abubuwan da ya gada na sana’a, karamci da jajircewar sa na cigaba za a tuna da su kuma za a girmama su har wasu lokuta masu zuwa.”
Ƙungiyar ta cigaba da cewa, “A cikin wannan lokaci mai cike da alhini, muna miƙa ta’aziyyar mu ga mai girma gwamna, da gwamnatin Jihar Kano da ɗaukacin iyalan Ɗantata, ‘yan kasuwa, da ɗaukacin al’ummar Kano baki ɗaya.”
Allah Ta’ala ya gafarta masa kurakuran sa, ya saka masa da Jannatul Firdaus, ya kuma bai wa iyalan sa, abokan sa da al’ummar Kano haƙurin jure wannan babban rashi da ba za a iya maye gurbin sa ba.
Alhaji Aminu Ɗantata dai ya rasu ne a Abu Dhabi da ke ƙasar Haɗaɗɗun Daulolin Larabawa (UAE) a jiya Asabar, kuma ana sa ran za a binne shi a Madina kamar yadda ya yi wasici. Shekarun sa 94 a duniya.