FITACCEN jarumin barkwanci a Kannywood, Mustapha Nabraska, ya kai wa surukin sa ziyarar kafin Babbar Sallah, a Katsina a jiya Juma’a, 16 ga Yuli, 2021.
Nabraska dai ya na auren Hajiya Amina, ɗiya ga fitaccen ɗan jaridar nan kuma marubuci, Malam Muhammad Ɗanjuma Katsina, wanda shi ne mawallafin jaridun yanar gizo na ‘Katsina City News’ da jaridar ‘Taskar Labarai’ da kuma mujallun ‘Matasa’ da ‘Katsina City News’.
A wannan hoto ga Nabraska nan a hagu tare da matar sa a tsakiya da kuma Malam Ɗanjuma ɗauke da ɗiyar su Nabraska.
Allah ya bada ladar ziyara, amin.
![]()






