WASU masu shirya finafinai ‘yan ƙasar Isra’ila za su shiga mako na biyu ana tsare da su a Nijeriya.
Jaridar ‘Times of Israel’ ta ruwaito a wani rahoto da mujallar Fim ta fassara cewa Yahudawan da ke zaune a ƙasar nan sun shaida mata cewa hukumomin Nijeriya ba su faɗa wa ‘yan fim ɗin takamaiman laifin da su ka aikata ba, sannan ba su samu lauyan da zai kare su ba.
‘Yan Isra’ila ɗin su ne Rudy Rochman, wanda ɗan gwagwarmayar tabbatar da kafuwar Isra’ila ne mai mabiya kusan 95,000 a Instagram, da mashiryin fim Andrew Noam Leibman da kuma wani ɗan jarida Ba’isra’ile kuma ɗan ƙasar Faransa, Edouard David Benaym.
An kama su ne a makon jiya lokacin da su ke ɗaukar wani shirin talbijin a yankin kudu-maso-gabashin Nijeriya.
Wasu kafofin yaɗa labarai a Nijeriya sun ce jami’an tsaro na farin kaya, wato DSS, sun kama Isra’ilawan tare da yi masu tambayoyi a ranar 9 ga Yuli a bisa zargin su na da alaƙa da ‘yan tawayen Biyafra.
A daren da aka kama su ɗin, ‘ya’yan ƙungiyar Yahudawa mazauna Nijeriya sun kira babban limamin su a Nijeriya mai suna Rabbi Israel Uzan wanda ke hutu a Faransa, sun sanar da shi halin da ake ciki.
Shi kuma Uzan, tare da Yahudawa mazauna Nijeriya, sun riƙa samar wa kamammun irin abincin ƙasar su da kuma kayan gudanar da addinin su.
“Mu nan mu na taimaka masu tare da taimaka wa iyayen su da haɗa su da masu faɗa a ji, da abinci saboda waɗannan yaran, da dukkan abin da su ke buƙata don gudanar da ibadar Shabbat, da kuma ‘tefillin’,” inji Uzan.
Jaridar ta ruwaito cewa ɗaya daga cikin mazan uku sun shigo Nijeriya ne da fasfo ɗin Faransa, yayin da sauran biyun su ka shigo da fasfunan Amerika. Hakan ya sa ofishin jakadancin Isra’ila ya kasa shiga cikin al’amarin da farko, a cewar wata majiya mai masaniya kan lamarin.
Jaridar ta ƙara da cewa wani abu da ya ƙara rikita al’amarin shi ne ofishin jakadancin Amerika ya rage ayyukan sa ranar Juma’a saboda halin tsaro, kuma bai bada wasu bayanai ba.
Ta ce za a yi Babbar Sallar Musulmi a mako mai zuwa, wanda hakan na nufin ofishin jakadancin ba zai koma aiki sosai da sosai ba har zuwa ranar 26 ga Yuli.
A cewar jaridar, iyalan mutanen da aka kama ɗin sun faɗa ran Laraba cewa wasu ‘yan siyasar Nijeriya sun “murɗa” batun bada kyautar littafin Attaura ga wasu mutane a ƙasar da nufin cewa su na goyon bayan ‘yan awaren Biyafra.
Yanzu haka littafin Attaura ɗin ya na hannun mutanen yankin da aka bai wa shi.

Jaridar ta ruwaito cewa waɗannan ‘yan Isra’ilan sun zo Nijeriya ne domin su shirya wani fim mai suna ‘We Were Never Lost,’ wato ‘Ba Mu Taɓa Ɓacewa Ba’, wanda shiri ne mai duban mabiya addinin Yahudawa a ƙasashen Afrika irin su Kenya, Madagaska, Uganda da Nijeriya.
Sun tashi daga filin jirgin sama na Ben Gurion da ke Tel Aviv a Isra’ila a ranar 5 ga Yuli, su ka sauka a Nijeriya washegari.
A cewar wasu ‘yan Nijeriya a yankin gabashin, jami’an tsaro sun kama mashirya fim ɗin ne a wani cocin addinin Yahudawa lokacin da ake tsakar gudanar da ibada a daren ranar Alhamis a wani ƙauyen Inyamirai mai suna Ogidi, daga nan aka kai su Abuja.
Jaridar ta ce Inyamirai su na kallon kan su a matsayin wata ƙabilar Yahudawa da ta ɓace.
A sanarwar da su ka fitar, iyalan waɗanda aka kama ɗin sun bayyana cewa mashirya fim ɗin sun tafi da kyaututtuka ga mutanen yankin da su ka karɓi baƙuntar su.
Da su ka iso Nijeriya, sun haɗu a makon jiya da wani shugaban ƙabilar Ibo, Eze Chukwuemeka Eri, su ka kai masa wani hoto cikin gilashi na Shiviti wanda aka yi a Birnin Ƙudus.
Haka kuma Rochman ya bada kyautar littafin Attaura ga wani ƙauyen Inyamirai wanda wani mai zane a bakin hanya ɗan ƙasashen Birtaniya da Isra’ila mai suna Solomon Souza ya tsara bangon sa.
“Mashirya fim ɗin sun yi tunanin zai kyautu su kai kyaututtuka da dama masu alamta al’adun Yahudawa ga al’ummomin da za su ziyarta” inji iyalan a sanarwar da su ka fitar, har su ka ƙara da cewa ɗaya daga cikin kyaututtukan shi ne littafin na Attaura.
“Abin baƙin ciki ne a ce wasu ƙungiyoyin siyasa waɗanda ba sa cikin gwamnati sun juya batun hotunan ‘yan fim ɗin na miƙa kyautar Attaurar ga mutanen ƙauyen tare da sauya ma’anar hakan saboda wasu dalilai nasu na son rai,” inji iyalan.
Su ka ƙara da cewa, “Waɗannan mutanen su na dagula manufofin mashirya fim ɗin a ƙoƙarin su na ƙirƙiro wata dangantaka da yanayin siyasar ƙasar a yayin da babu irin wannan dangantakar.
“Waɗannan mutanen da ke taka rawa a siyasance sun ɗauki ƙaramar magana ta nuna kirki sun murɗa ta a ƙoƙarin ƙirƙiro wata manufa ta daban.”
Wani ɗan’uwan ɗaya daga cikin kamammun ya faɗa wa jaridar ta ‘The Times of Israel’ a ranar Talata cewa wasu ƙungiyoyin ‘yan awaren Biyafra da ke soshiyal midiya sun yi amfani da zuwan waɗannan mashirya fim ‘yan Isra’ila su na faɗin cewa magoya bayan su ne.
Iyalan kamammun su ka ce, “An tsara shirin fim ɗin ne domin a wayar da kan masu kallo game da yanayin addini da al’adu na wasu al’ummomin Yahudawa da ba a san da su sosai ba. Burin su shi ne su tattauna da membobin al’ummomin Yahudawa da ke zaune a ƙasashe daban-daban na Afrika, tare da al’ummomin Yahudawa da ke Chaina, Indiya, Afghanistan da sauran wurare.”
Su ka ce, “Wannan shirin talbijin ɗin ba ya da nufin yin wata magana da ta danganci siyasar ƙasashen da ake ɗaukar fim ɗin a cikin su, ko a ce masu shirya fim ɗin su na goyon bayan wasu ƙungiyoyin siyasa. Mashirya fim ɗin su na zuwa ne a matsayin baƙi masu ziyartar ƙasar tare da al’ummomin ta daban-daban – babu wata ɓoyayyiyar manufar siyasa.”
Jaridar ta ce mashirya fim ɗin su na sane da damuwar da ke akwai game da siyasar ɗaukar wannan fim kan al’ummar Igbo. A ranar Alhamis da ta gabata, shafin shirin na ‘We Were Never Lost’ da ke Facebook ya ce: “Ba mu ɗaukar kowane matsayi kan kowace ƙungiyar siyasa domin ba mu zo a matsayin ‘yan siyasa ba ko a matsayin wata tawaga ta gwamnati.”
Jami’an tsaro sun ɗan saki ɗaya daga cikin waɗanda ke tsare ɗin, Benaym, ran Talata da yamma, su ka miƙa shi ga ofishin jakadancin Faransa a Abuja saboda wani dalili na rashin lafiya da ba a bayyana ba, kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje ta Isra’ila ya faɗa wa ‘The Times of Israel’ ran Laraba.
Iyalan sun tabbatar da haka, su ka ce, “A wata alama ta sassauci, ‘yan DSS sun ƙyale Ofishin Jakadancin Faransa ya karɓi Edouard David Benaym ran Talata da dare saboda ya samu wata kulawa saboda rashin lafiya, da niyyar a mayar da shi hannun DSS washegari domin ci gaba da binciken.”
Wani abokin iyalan ɗaya daga cikin kamammun ya faɗa wa jaridar cewa wani tsohon ministan Isra’ila, Ayoub Kara, ya hau jirgi ya tafi Nijeriya don ya taimaka wajen tattauna matsalar, amma kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje ya ce a’a, da man Kara ya na cikin Nijeriya lokacin da matsalar ta taso, kuma babu hannun sa ko kaɗan a aikin diflomasiyyar da ake yi kan wannan batu.
Jaridar ta ce Kara bai ce komai ba lokacin da ta nemi ya ce wani abu.
Iyalan su ka ce, “Mu na bakin ƙoƙarin mu sosai tare da ofisoshin jakadancin Amerika, Isra’ila da Faransa a kan lamarin, kuma mu na godiya matuƙa da kulawar da su ka ba maganar. Shigowar su ciki ta taimaka gaya wajen kyautata zaman mashirya fim ɗin a inda su ke a tsare – wanda ya haɗa da kai masu abincin ‘kosher’ wanda shugaban addinin mu da ke ƙasar ya shirya.
“Mu na fatan DSS za su gaggauta ɗaukar matsayi kan abin da hujjoji su ka tabbatar – wato cewa mashirya fim ɗin ba su da wata manufa ta siyasa, kuma a sake su ba tare da wani ɓata lokaci ba.”
Jaridar ta ce a watan Janairu da ya gabata, rikici ya ɓarke tsakanin mayaƙan ‘yan aware na ƙungiyar IPOB da jami’an tsaron Nijeriya, kuma har yanzu ana rikicin.
Ta ce a baya, lokacin da Inyamirai su ka bayyana ɓallewar su daga Nijeriya a cikin 1967, sai da aka shafe watanni 30 ana tafka yaƙin basasa wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum miliyan ɗaya.
A cikin 2018, magoyin bayan sake ɓallewar Biyafra, Nnamdi Kanu, ya yi wata sanarwa a rediyo inda ya ce ya na cikin Isra’ila kuma ƙasar Yahudawan ce ta taimaka masa har ya tsere.
Kanu, wanda a da dillalin gidaje ne a London, shi ne shugaban IPOB da haramtaccen gidan rediyon asiri na ‘Radio Biafra’. Ya na iƙirarin cewa Igbo, waɗanda su ne ƙabila mafi rinjaye a kudu-maso-gabashin Nijeriya, al’ummar Yahudawa ce da su ka ɓace kuma burin sa shi ne ya mayar da su zuwa “ƙasar alƙawari” ta Biyafra.
Yanzu haka Kanu na fuskantar shari’ar cin amanar ƙasa a Nijeriya. A cikin Yuni 2021 ‘yan sandan ƙasa da ƙasa (Interpol) su ka cafke shi a ƙasar Jamhuriyar Czech.
*Ma’aikatan AFP da ‘Times of Israel’ su ka haɗa wannan rahoto, kuma mujallar Fim ta fassara shi.
![]()






