• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Nura M. Inuwa: Abin da ya sa na gaza sakin album a Fabrairu

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
March 8, 2021
in Mawaƙa
0
Nura M. Inuwa: Abin da ya sa na gaza sakin album a Fabrairu
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCEN mawaƙi Nura M. Inuwa ya bayyana dalilin sa na rashin fitar da fayafaye biyu na waƙoƙin sa a ƙarshen Fabrairu kamar yadda ya alƙawarta.


A watan jiya dai fastocin kundin waƙoƙin sa sun karaɗe soshiyal midiya wanda ya sa aka yi tsammanin mawaƙin zai saki kundaye biyu na waƙoƙin a ƙarshen watan kamar yadda ya yi wa masoyan sa albishir a cikin wata hira da ya yi da mujallar Fim.


Sai ga shi har an haura mako ɗaya a cikin sabon wata amma an ji shiru.


Masoyan Nura sun zaƙu su ji sababbin waƙoƙin sa ne domin an ɗauki tsawon shekaru biyu su na jira.


Ana haka ne kwatsam, sai mawaƙin ya fito da wata sanarwar ban-haƙuri game da gazawar sa kan wannan al’amari a shafin sa na Facebook, amma bai bayyana dalili ba.


Kan haka ne mujallar Fim ta tuntuɓe shi domin jin dalilan da ya sa bai saki waɗannan album ɗin nasa guda biyu ba kamar yadda ya alƙawarta. 


A tattaunawar sa da wakilin mu, Nura M. Inuwa ya ce, “Dalilin da ya sa ban saki albam ɗi na ba masu suna ‘Ni Da Ku’ da kuma ‘Lokaci’ shi ne mu na so ya kasance lokaci guda mun sake su a gari a kan sidi da kuma sauran guraren da mu ke so na yanar gizo, yanda zai zama kowa ya samu ba tare da an samu jinkiri ba ta yadda wasu za ka ga sun riga wasu samu; misali, za ka ga akwai da dama daga cikin masoya na wanda ba sa iya ɗaukar abu daga kan yanar gizo. 


“Wannan dalilin ne ya sa mu ke so mu je har gurin masu ‘downloading’ da kuma ‘yan kasuwa mu tattauna domin mu sake su a kowace kafa a kuma lokaci guda.


“Sannan akwai matsalar da mu ka samu daga kamfani na rashin kammala abubuwa da dama na wannan kundin nawa.”


Shin da ma can ba su gama shiryawa ba amma ya bayyana ƙarshen Fabrairu a matsayin lokacin da za su saki kundayen? Sai ya amsa da cewa: “Mun shirya da kuma sanin cewa lokaci zai ishe mu mu yi har mu cimma saki a ƙarshen watan na Fabrairu. Da mu ka tattara mu ka kuma tura kamfani, sai ya zamana mun samu wata tangarɗa. Shi ya sa dole aka samu ɗan bambanci. 


“Kuma a yau ne mu ke sa ran jin ta bakin shi kamfani kan wannan al’amari da kuma lokacin da za su ƙarasa kawo mana kayayyakin mu. 


“Sannan masoya na ba na jin hakan zai sa su ƙosa domin yardar da su ke da ita a kai na ba na jin za ta ba su wani sarewa a kan haka. 


“Amma dai na san da cewa masoya na sun  ƙagu su ji waƙoƙi na. Da haka ne kuma na ke ƙara ba su haƙuri kan wannan tsaiko da aka samu.”


Bugu da ƙari, Nura ya bayyana cewa, “Komai idan ɗan’adam ya nufa zai yi idan Allah bai amince ba dole ya haƙura, kamar yadda mu mu ka tsara cewa lokaci kaza za mu yi abu cikin yaddar Allah, kuma bai nufa ba. Ina fatan jinkirin ya zama alkairi.


“Sannan kuma masoya na su ci gaba da jira, don ko a yau kamfani ya ba mu tabbacin cewa ya kammala komai.


“Ina kuma bada tabbacin da yardar Allah a cikin watan Maris ɗin nan da mu ke ciki komai zai kammala kuma kowa zai samu waƙoƙi na na wannan shekarar  in dai ya buƙaci haka.”

Nura M. Inuwa ya na waƙa a wajen wani bikin aure
Tags: Hausa musicKannywoodNura M. Inuwawakokin Hausa
Previous Post

Yarjejeniya: Afakallah zai daina kama ‘yan fim haka barkatai

Next Post

Iyan-Tama: Har yanzu da ni ake damawa a Kannywood

Related Posts

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi
Mawaƙa

Hotunan Ranar Farko ta taron tunawa da Makaɗa Kassu Zurmi

April 19, 2025
Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa nake rubuta littafin rayuwa ta – Ala

October 28, 2024
Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala
Mawaƙa

Abin da ya sa na koma yin waƙa da kayan kiɗan gargajiya – Aminu Ala

July 16, 2024
Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara
Mawaƙa

Nazarin waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ta Dauda Kahutu Rarara

May 13, 2024
Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 
Mawaƙa

Waɗansu waliyyai a Nijar da Nijeriya 

December 7, 2023
Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala
Mawaƙa

Ɗaliban Hausa ‘yan ƙasar Sin sun ziyarci mawaƙi Aminu Ala

December 3, 2023
Next Post
Iyan-Tama: Har yanzu da ni ake damawa a Kannywood

Iyan-Tama: Har yanzu da ni ake damawa a Kannywood

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!