DAGA yanzu, Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ba za ta sake kama duk wani ɗan fim ba har sai ta tuntuɓi kwamitin ladabtarwa da Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) za ta kafa cikin gaggawa.
Wannan ya na daga cikin sharuɗɗan da ɓangarorin biyu su ka cimmawa a wani zama da su ka yi a ranar Laraba, 3 ga Maris, 2021, a Kano.
Sun yi zaman ne domin kawo ƙarshen matsalolin da ke ci wa ‘yan fim tuwo a ƙwarya, musamman ma yadda hukumar ke kama su ta na gurfanar da su a kotu a bisa laifi iri daban-daban da ta ke zargin su da aikatawa.
Kamu na baya-bayan nan shi ne wanda hukumar ta yi wa fitaccen darakta Mu’azzam Idi Yari.
‘Yan fim da dama su na danganta kamun da hukumar ke yi masu da dalilai na siyasa ko son rai.
Kakakin MOPPAN na ƙasa, Malam Al-Amin Ciroma, ya shaida wa mujallar Fim cewa zaman ya ɗauki aƙalla sa’o’i huɗu kuma ya samar da nasara gami da ingantacciyar hanyar wanzar da fahimta da samar da mafita ga waɗansu manyan matsaloli da ‘yan fim ke kokawa da su game da hukumar.
Ya ce tun da fari dai, shugaban hukumar, Malam Isma’ila Na’Abba (Afakallah), ya karɓi tawagar ƙungiyar cikin mutunci da girmamawa.
Haka kuma ya bayyana muradin hukumar tasa na tabbatar da nasarar daidaita al’amura a masana’antar shirya finafinai da ɓangarorin ɗab’i da sauran fuskoki da gwamnati ta ɗora wa hukumar alhakin gudanarwa.
A nasa ɓangaren kuma, Shugaban MOPPAN na ƙasa, Dakta Ahmad Sarari, ya bayyana dalilan da su ka tilasta ziyarar dangane da manyan koken da ‘yan fim ke yi ga hukumar a ko da yaushe.
A cewar sa, dukkanin ɓangarorin biyu su na buƙatar junan su.
A yayin zaman, bayan doguwar tattaunawa, an cimma wasu matsaya kamar haka:
1. Hukuma ba za ta sake kama kowa ba har sai ta tuntuɓi kwamitin ladabtarwa (Disciplinary Committee) da MOPPAN za ta kafa cikin gaggawa. Ma’ana, MOPPAN ce ke da damar fara yi wa ɗan ta gargaɗi muddin ya yi laifi, sannan ta tabbatar ya gyara, kuma ya bi doka tukunna a tashin farko. Amma idan ya bijire, ya ƙi bin doka, ba za ta hana hukuma ɗaukar matakan da su ka dace a kan shi ba.
2. Daga yanzu duk wanda ya ke neman izinin gudanar da wani aikin fim, wato ‘film shoot permit’ a Jihar Kano, tilas ne ya kai wa hukumar tace finafinai takardar kasancewar rukunin ƙungiyar sa daga MOPPAN. Ma’ana, ya zama memba na ƙungiyar.
3. Duk wanda kai zai fim ko waƙa, ko wani aiki nasa domin a tace, tilas sai ya nuna amincewa (‘clearance’) daga MOPPAN.
4. Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ba za ta sake yi wa kowane ɗan masana’antar Kannywood rajista ba har sai ya kawo shaidar kasancewar sa ɗan ƙungiyar MOPPAN ne.
5. MOPPAN da hukumar sun cimma yarjejeniyar haɗin gwiwar shirya tarukan bita gami da ƙara wa juna sani da kuma koyar da da sana’a ga ‘yan fim ta dukkanin ɓangarorin sana’ar su.
Ya na da kyau duk mai sana’ar fim a Nijeriya ya fahimci cewar ita kan ta Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa (NFVCB), tuni har ta yanke hukuncin daina yin kowace irin mu’amala da duk wani ɗan fim sai wanda ya yi rajista da ƙungiya kuma ya sami ‘clearance’ daga ƙungiyar da hukumar ta yarda da ita.
MOPPAN dai ta na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da NFVCB ta amince da su.
A ƙarshen zaman da aka yi, Afakallahu ya yi wa ‘yan fim baki ɗaya fatan alheri, sannan ya yi addu’ar Allah ya ba su damar haɗa kan su a ko da yaushe.







