KWALEJIN Koyon Larabci da Shari’a ta Aminu Kano da ke Kano ta karrama mawaƙi Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara) da satifiket na musamman saboda gudunmawar da ya ke bayarwa ga harshen Hausa.
An karrama shi ne a lokacin wani taro da makarantar ta shirya a Kano domin neman gudunmawar jama’a don ta kyautata tsarin karatun ta.
A lokacin da ya ke miƙa kyautar karramawar ga Rarara, Shugaban makarantar, Alhaji Abubakar Balarabe Jakada, ya bayyana cewa makarantar ta karrama Rarara ne saboda yadda ya ke bai wa harshen Hausa gudunmawa, kuma waƙoƙin sa sun zama abubuwan nazari a makarantun ƙasar nan.

Ya ce kuma ce makarantar ta buƙaci taimakon al’umma ne domin ta gina wani sashe na aikin jarida don inganta karatu a makarantar.
A nasa jawabin, Rarara ya bayyana cewa ƙungiyar sa ta 13×13 ta bayar da gudunmawar naira miliyan ɗaya sannan kuma a karan kan sa ya ba da rabin miliyan domin taimakon ilimi.
Rarara ya yi wa makarantar godiya tare da yi wa ɗaliban ta fatan alheri.