• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, August 10, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rasuwar jarumar Kannywood Wasila Isma’il ta girgiza jama’a

* Za a yi jana'izar ta gobe da safe a Kaduna

by ABBA MUHAMMAD
May 24, 2026
in Labarai
0
Rasuwar jarumar Kannywood Wasila Isma’il ta girgiza jama’a

Marigayiya Wasila Isma'il

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ALLAH ya yi wa fitacciyar jarumar Kannywood, Wasila Isma’il, rasuwa a yau Lahadi, lamarin da ya girgiza ba ma masana’antar finafinan Hausa kaɗai ba har ma da sauran al’umma.

Wasila ta rasu a yammacin yau a Asibitin FOMWAN da ke unguwar Badarawa, a garin Kaduna, sakamakon ciwon suga da ta daɗe tana fama da shi, sai kuma bugun zuciya da aka ce shi ne ajalin ta.

Shekarun ta kimanin 46 a duniya.

Wasila ta rasu ta bar ‘ya’ya huɗu, mata uku da namiji ɗaya, waɗanda suka haifa tare da tsohon mijin ta, wato jarumi kuma darakta Al-Amin Ciroma.

‘Ya’ya biyar suka haifa, amma namiji ɗaya ya rasu tun tuni.

Ita da Ciroma, wanda fitaccen ɗan jarida ne, sun rabu shekaru uku da suka gabata bayan sun shafe kusan shekaru 21 suna zaman aure.

Ƙasa da shekara ɗaya kafin mutuwar auren, wato a ranar Alhamis, 6 ga Oktoba, 2022 Ciroma da Wasila suka yi bikin cikar su shekara 20 da aure.

Rabuwar auren, wadda mujallar Fim ce ta fara ba da labarin shi a ranar 4 ga Yuli, 2023, ta girgiza masu karatu.

Masoyan jaruman biyu sun yi ƙoƙarin sasanta su domin su koma auren, amma abin ya ci tura.

Daga bisani Wasila ta sake dawowa harkar fim, inda ta cigaba da ƙoƙari wajen bayar da gudunmawa a fannoni daban-daban na masana’antar ta Kannywood tare da nuna jajircewa wajen tallafa wa cigaban masana’antar.

Wata majiya ta ce mutane da dama da suka gan ta a jiya ba su kawo mata mutuwa kusa ba domin an gan ta tana harkokin ta cikin ƙoshin lafiya, har ma ta ziyarci mutane a gidajen su.

Rasuwar tata ta girgiza masana’antar Kannywood matuƙa. ‘Yan fim da sauran jama’a suna ta bayyana alhinin su tare da yi mata addu’a, musamman a soshiyal midiya.

Ciroma ya wallafa alhinin sa a shafin sa na Facebook, inda ya ce: “Innaa lillahi wa innaa ilaihi raaji’uuun. Allah Ta’ala Ya yi wa Malama Wasila Ismail Rasuwa.
Allah Ya gafarta ma ta, mu ma Allah Ta’ala Ya sa mu gama lafiya Ameeeen.”

Saƙon ya ja hankalin jama’a matuƙa, inda aka dinga yi wa marigayiyar addu’ar samun rahama.

An faɗa wa mujallar Fim cewa ba za a yi jana’izar marigayiyar a yau ba saboda yamma ta yi sannan ga garin da hadari.

Sai gobe za a yi jana’izar da ƙarfe 10:00 na safe a gidan su da ke Shagari Junction da ke Badarawa, kusa da tsohon ofishin ubangidan Wasila, wato Yakubu Lere.

Allah ya jiƙan Wasila, ya gafarta mata kurakuran ta, ya sanya Aljannar Firdausi ta zama makoma a gare ta, sannan ya kyautata rayuwar ‘ya’yan ta, amin.

Loading

Tags: Al-Amin CiromarasuwaWasila Ismail
Previous Post

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

Next Post

Ɗimbin jama’a suka halarci jana’izar Wasila Isma’il

Related Posts

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama
Labarai

Fitaccen mawaƙin siyasa Muhammadu Buhari ‘Kosan Waka’ ya kwanta dama

August 2, 2026
Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11
Labarai

Yadda gwajin ƙwayoyin halitta na jini ya kawo ƙarshen auren Adam A. Zango da Maimuna Musa bayan watanni 11

August 1, 2026
Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano
Labarai

Jami’an gwamnati sun yi zama da Kannywood domin fara aiwatar da shirin ba da inshorar lafiya kyauta ga ‘yan fim na Kano

July 15, 2026
Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu
Labarai

Kannywood tana buƙatar farfaɗo da gidajen sinima domin bunƙasa tattalin arzikin ƙirƙira – Sani Mu’azu

July 14, 2026
A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti
Labarai

A hira da mujallar Fim, mawaƙi Ado Gwanja ya aiko da saƙo ga masoyan sa daga gadon asibiti

July 9, 2026
Next Post
Ɗimbin jama’a suka halarci jana’izar Wasila Isma’il

Ɗimbin jama'a suka halarci jana'izar Wasila Isma'il

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!