MAGAJIN jarumin barkwanci a Kannywood, marigayi Rabilu Musa Ɗanlasan (Ibro), wato Hannafi Rabilu Musa, ya roƙi jama’a da su ci gaba da yi wa mahaifin sa addu’a kamar yadda su ka saba.
Ya yi wannan roƙo ne a Instagram a yau Asabar, 10 ga Disamba, 2022, wanda a yau ɗin ne mahaifin nasu ya cika shekara takwas cif da rasuwa.
Hannafi ya ce, “Assalamu alaikum warahamatullahi ta’ala wa barakatuhu. Suna na Hannafi Rabilu Musa Ɗan Ibro. Yau ga rana ta zo, yau 10 ga watan 12, 2022, shi ne ya yi daidai da mahaifi na ya cika shekara 8 da rasuwa.
“Da ma na sani jama’a aikin ku ne ko da yaushe ku na yi wa mahaifi na addu’a a kan Allah ya jiƙan sa, Allah ya gafarta masa, to yau ma mu na buƙatar ku sa shi cikin addu’ar ku, Ubangiji Allah ya sabunta masa rahama.
“Ba ma shi kaɗai ba, duk wani Musulmi da ya mutu a duniyar nan Ubangiji Allah ya jiƙan sa, Allah ya gafarta masa, Allah ya sa ya huta, Allah ya yafe masu kurakuran su don arziƙin Annabi Muhammadu (S.A.W), kuma Ubangiji ya sa mu ƙara cin arziƙin Annabi Muhammad (S.A.W) a ko da yaushe.”

Ɗan marigayin ya ƙara da cewa, “Ni babu abin da zan ce wa al’umma sai dai godiya. Saboda a ko da yaushe idan na hau soshiyal midiya, abin da na ke gani kenan kuma na ke jin daɗin sa. In dai zan hau zan ga Allah ya jiƙan mahaifin ka, Allah ya gafarta masa, Allah ya sa ya huta. In dai zan ga abin nan, ina jin daɗin abin nan. Na gode, Ubangiji Allah ya bar zumunci, na gode sosai.”
A wannan rana jama’a da dama sun yi wa Ibro addu’a, musamman abokan sana’ar sa da kuma masoyan sa.
Tun a jiya Juma’a, 9 ga Disamba, 2022, Hannafi ya ɗora hoton mahaifin nasa, sannan ya rubuta cewa, “Aslm al’umma kamar yadda aka saba yi wa mahaifina addu’a kullum da kuma duk shekara ku sani cewa yau mu na 9/12/2022, gobe kuma mu na 10/12/2022, shi ne lokacin da mahaifi na ya cika shekara takwas (8). Mu na ƙara gdy ga al’umma da su ci gaba da yi wa ilahirin dukkan Musulman duniya da su ka riga mu gidan gaskiya ngd ngd. Gobe zan yi sabon posting in Allah ya kai mu.”
Ibro dai ya rasu ne a ranar Laraba, 10 ga Disamba, 2014.