• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 23, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Shekaru 15 da aure: Jarumar Kannywood Muhibbat Abdulsalam da darakta Hassan Giggs sun yi hamdala

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
June 28, 2023
in Ranar Murna
0
Muhibbat Abdulsalam da maigidan ta, Malam Hassan Giggs, cike da murna

Muhibbat Abdulsalam da maigidan ta, Malam Hassan Giggs, cike da murna

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

A YAU ne daraktan Kannywood Hassan Giggs da matar sa, tsohuwar jaruma Muhibbat Abdulsalam, su ka cika shekaru 15 cur da aure, don haka su ka shiga soshiyal midiya su ka bayyana farin ciki tare da hamdala.

A wani saƙo da ta wallafa a Facebook da Instagram kan wannan muhimmin zango da su ka kawo, Hajiya Muhibbat ta yi godiya ga Allah da ya nuna masu wannan muhimmin zango, inda su ka zauna a matsayin ma’aurata tare da samun ƙaruwar ‘ya’ya.

Cikin zumuɗi, ta ce: “Alhamdu lillah, alhamdu lillah, alhamdu lillah. Ikon Allah ne da kuma addu’ar iyaye. Allah na gode maka. Godiya mara misaltuwa.

“Allah na gode maka da ka ba ni ikon zama da miji na na tsawon wannan shekaru.

Giggs da Abdulsalam da ‘ya’yan su uku

“Ya Allah na roƙe ka don darajar Manzon ka Allah ka sa mutuwa ce za ta raba mu. Ya Allah ka yi wa zuri’ar mu albarka.”

Daga nan tsohuwar jarumar wadda a yanzu ‘yar kasuwa ce mai kamfanin ‘Muhibs Ultra Shine Formula’ inda ta ke sayar da kayan gyaran jiki da na gyaran aure, ta miƙa saƙon godiya ga mijin nata saboda mara mata da ya ke yi. A turance ta rubuta cewa: “@hassan_giggs thanks a lot for always supporting me. May Allah reward you with Jannatul Firdausi, amin. 15 years is not a day job.”

Muhibbat ta wallafa hotuna kamar shida na ita da Giggs da ‘ya’yan su waɗanda su ka ɗauka musamman don murnar zagayowar wannan lokaci.

Shi ma Giggs ya wallafa wani hoto da aka ɗauke su tare da jarumai irin su su Hajara Usman da Fati Yola a ranar auren su a soshiyal midiya.

Hassan Giggs da iyalin sa

Auren Giggs da Muhibbat, wanda aka ɗaura a ranar 28 ga Yuni, 2008, ya na daga cikin aurarrakin ‘yan fim da ake ba da misali da su na yadda su ka yi shekaru masu yawa su na zaune lafiya ba tare da sun rabu ko kuma an ji kan su ba.

Allah ya albarkaci auren da kyawawan ‘yan mata guda uku.

Hassan Giggs da Muhibbat Abdulsalam da yaran su
Sai godiyar Allah: Hassan Giggs da Muhibbat Abdulsalam
Iyalan Giggs

Loading

Tags: Hassan GiggsMuhibbat AbdulsalamWedding Anniversaryzagayowar ranar aure
Previous Post

Rasuwar marubuci Auwal Garba Ɗanborno ta girgiza Arewa

Next Post

Ta’aziyyar Auwalu Garba (24/12/1978-25/06/2023)

Related Posts

MC Kabir Bahaushe zai ƙara aure ran Asabar
Ranar Murna

MC Kabir Bahaushe zai ƙara aure ran Asabar

July 22, 2025
Furodusa a Kannywood, Shu’aibu Yawale ya aurar da ‘ya’ya biyu
Ranar Murna

Furodusa a Kannywood, Shu’aibu Yawale ya aurar da ‘ya’ya biyu

July 18, 2025
Furodusa a Kannywood, Rabi’u Koli da A’isha sun zama ɗaya
Ranar Murna

Furodusa a Kannywood, Rabi’u Koli da A’isha sun zama ɗaya

July 16, 2025
Ranar Murna

Furodusa a Kannywood, Rabi’u Koli zai yi aure ranar Asabar

July 10, 2025
Al-Ameen, Haidar na shirin Daɗin Kowa, ya zama angon Walida
Ranar Murna

Al-Ameen, Haidar na shirin Daɗin Kowa, ya zama angon Walida

June 29, 2025
Haihuwa ta 14: Mawaƙi Abubakar Yarima ya samu Muhammad Sani
Ranar Murna

Haihuwa ta 14: Mawaƙi Abubakar Yarima ya samu Muhammad Sani

June 19, 2025
Next Post
Ta’aziyyar Auwalu Garba (24/12/1978-25/06/2023)

Ta'aziyyar Auwalu Garba (24/12/1978-25/06/2023)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!