ALLAH ya azurta tsohuwar jarumar Kannywood Zainab Umar, wadda aka fi sani da Zainab Raga, da samun ƙarin haihuwa ta ‘ya mace.
Zainab ta haihu ne a ranar Asabar 6 ga Satumba, 2025.

An yi taron raɗin suna a ranar Asabar da ta gabata a gidan mijin ta da ke unguwar Hotoro a Kano, inda ‘yan’uwa da abokan arziki suka taru domin taya ta murna.
‘Yan fim da dama sun halarci taron sunan, irin su Sadiya Gyale, Fauziyya Sani Maikyau, da sauran su.
Zainab ta yi yayin ta a industiri a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2016. Fim ɗin ‘Raga’ da ake mata inkiya da shi yana ɗaya daga cikin manyan finafinan da ta yi.


![]()







