MUTUMIN nan wanda ya yi ƙarar Rahama Sadau a wajen ‘yansanda a kwanan baya, wato Alhaji Lawal Muhammad Gusau, a yau ya maida akalar sa ga wata fitacciyar jarumar ta Kannywood, Nafisat Abdullahi, a kan irin shigar da ta ke yi.
Mutumin, wanda ya rubuta buɗaɗɗiyar wasiƙa ga Nafisar, ya ce shigar da ta yi a wasu hotuna da ta ɗauka a ƙasar Masar kwanan nan ta saɓa wa addinin Musulunci, kuma idan ba ta cire su ba to zai maka ta a kotu.
Idan kun tuna, Lawal Gusau ya cinna wa Rahama Sadau ‘yansanda a kan wata shiga da ta yi wadda ta jawo ka-ce-na-ce musamman bayan wani arne ya aikata saɓo ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu (SAW).
Sai da ta kai Sufeto Janar na ‘Yansanda ya ba kwamishinan sa na Jihar Kaduna umurnin ya binciki jarumar.
Amma daga baya maganar ta kwaranye bayan ‘yansanda sun ƙi yarda su ɗau matakin da ya ke so bayan sun ɗan fara yi wa jarumar barazana da gayyata.
A wannan karon, Lawal Gusau, wanda ɗan kasuwa ne, wasiƙa ya rubuta wa Nafisa Abdullahi.
Wasiƙar, wadda ta shigo hannun mujallar Fim, ya rubuta ta ne bayan wasu hotuna da jarumar ta saka a shafin ta na Instagram a ranar 8 ga Disamba, 2020.
Hotunan na ziyarar buɗe ido da jarumar ta kai ne a wajen dalar rufe matattu (pyramids) da ke Giza, a bayan birnin Alƙahira.
Ga dai abin da ya ke cewa a cikin wasiƙar sa ga Nafisat Abdullahi:
“Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa gare ki, mai suna a sama, dangane da izgilanci da ki ka fara furtawa tun daga watan Fabrairu, 2020, a lokacin da Ibrahim Rufa’i (Deezell) ya saki hotunan tsiraici na Maryam Booth wanda a lokacin a matsayin ki na babbar aminiyar Maryam Booth, a maimakon ki yi Allah wadai da faruwar wannan abu, sai ki ka fito ki ka ce a kafafen sada zumunta na zamani, ki ka ce za ki saki hotunan ki ga al’ummar Annabi Muhammad (SAW) cikin kamfai (dros/pant) da rigan nono a bakin kududdufin ninƙaya (swimming pool).
“Duk wata ‘ya mace Musulma ba za ki zama abin koyi gare su ba. Wannan abu ya yi mani ciwo matuƙa.
“Abin koyi a nan, ki yi koyi da Fati Washa wadda al’ummar Musulmi sun jinjina mata domin ta fito a kafafen zumunta na zamani ta yi kalmar shahada, furucin ta na farko don nuna nadama da matuƙar ɓacin rai game da abin da babbar aminiyar ta ta yi, mai suna Rahama Sadau, wanda sanadiyyar abubuwan da su ka faru kwanakin baya a yanzu ita Rahama Sadau ta gane cewa da uba ake ado ba da sutura ba.
“A daidai wannan ga, saƙon mu gare ki shi ne mun ga hotunan da ki ka saki a kafafen zumunta na zamani cikin tsiraici tun daga watan Nuwamba, 2020 har zuwa yau, hotunan da ki ka ɗauka a birnin Alƙahira (Egypt) don ki nuna kyawun surar ki.
“Don inda ki ke a birnin Alƙahira duk kyawun ki, ba ki kai mutanen Annabi Yusuf ba.
“Mu na son ki sani cewa a wannan birnin da ki ka ɗauki hotuna na tsiraici, a nan aka yi Annabi Yusuf (AS), wanda kyan ga baki ɗayan sa Allah ya kasa kashi biyu ne, wanda an ba duk duniya kashi ɗaya, ciki har da wanda ki ke taƙama da shi, ɗaya kashin kuma an bai wa Annabi Yusuf (AS), amma bai taɓa kauce ma hanya ba. Kin dai ji labarin abin da ya faru tsakainin Annabi Yusuf (AS) da matar Sarkin Masar (Zaliha) inda ta neme shi don saɓa Ubangiji, kuma ya ƙi.
“Don haka, shi Musulmi na gaskiya ya na amfani da kyawun sa ne wajen biyayya ga dokokin Allah da kuma godiya da ni’imomin da Allah ya yi masa.
“A Ingila (England), bayan kin baro birnin Alƙahira (Egypt), babu wanda za ki burge, nan ma kuma ki ka ci gaba da yaɗa hotunan batsa har ki na alfahari da cewa ki na cikin birnin Ingila.
“Don haka, mu a tunanin mu abin da ya faru ga Rahama Sadau ya kamata ya zama darasi gare ki.
“Shawarar mu shi ne kar ki bari a sanadiyyar hotunan ki ya zama sanadiyyar wani ya sake ma Musulmi ko Annabi Muhammad (SAW) maganar da bai dace ba. Don haka, mun umarce ki da ki yi saurin janye hotunan ki a kafafen sada zumunta na zamani don kauce ma abin da zai je ya dawo, in kuma ba haka ba, ki shirya haɗuwar mu a kotun Musulunci nan bada daɗewa ba in-sha Allahu.

“Ki ƙara sani cewa duk abin da ki ke taƙama da shi, ki sani cewa ki na cin albarkacin arewacin Nijeriya kuma a matsayin ki na Musulma, kuma ‘yar wasan kwaikwayon Hausa da ki ke yi da harshen Hausa don haka waɗannan abubuwa guda uku da ki ke cin albarkacin su, ya kamata ki yi hattara. Kuma kuma ki san cewa addinin Musulunci ba abin wasa ba ne, haka kuma Arewa na da al’adu kyawawa abin koyi ga kowa.
“Jan kunne a nan shi ne Bahaushe ya ce sai bango ya tsage ƙadangare ke samun wurin shiga. Don a sanadiyyar abubuwan da ku ke yi ne ake ma addinin Musulunci izgilanci.
“A saƙon tuni da ya tura wa jarumar, Lawal Gusau ya ce idan ya kai ta kotu zai nemi a soke kamfanin ta na Nafs Entertainment ne bisa iƙirarin wai ta na amfani da shi ta na aikata baɗala.
Shi dai Gusau, ya yi suna wurin maka duk wani wanda ya ke ganin bai yi daidai ba a kotu wanda hakan ya sa wasu na masa kallon ɗan neman suna. Amma shi kuma a ɓangaren sa ya ce ya na ƙoƙarin kawo gyara ne a cikin al’umma.
Mujallar Fim ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Nafisa amma hakan ya faskara domin mun masa samun ta a waya.