• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yadda shigowar Netflix za ta sauya al’amurra a Kannywood, inji darakta Kamal S. Alƙali

* Za a daina yin fim barkatai, inji shi

by ABBA MUHAMMAD
March 21, 2024
in Labarai
0
Yadda shigowar Netflix za ta sauya al’amurra a Kannywood, inji darakta Kamal S. Alƙali

Kamal S. Alƙali

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƊAYA daga cikin manyan daraktoci kuma marubuta a Kannywood, Malam Kamal S. Alƙali, ya bayyana cewa shigowar da manhajar Neflix ta yi a Kannywood za ta sauya fasalin yadda ake shirya fim a masana’antar.

A yayin da ya nuna farin cikin sa da zuwan Netflix ɗin, ya kuma faɗi dalilin da ya sa aka rage ganin finafinan sa.

A wata zantawar musamman da ya yi da mujallar Fim, Kamal ya ce, “Na yi farin ciki da Allah ya kawo wata manhaja, Netflix, wadda a yanzu ne rubututtuka na za su yi tasiri. Domin akwai misalai da dama da su ka gabata na finafinai da su ke labari ne mai matuƙar ƙarfi, ta yadda ba kowa ya ke fahimtar su ba.

“So, kullum ƙwaƙwalwa ta tana yin gaba da abin da ake kallo, ina yin fim wanda na yi tunani a zuciya ta, wanda yake ko almara ko kuma wani irin fim wanda yake da sarƙaƙiya, ta yadda mai ƙaramin tunani ba zai iya fahimta ba, a taƙaice kenan.”

Ya ci gaba da cewa, “An daina yin fim barkatai, muna fatan haka. Kuma da ma shi fim, ba shi da tsarin barkatai kamar ƙwadago – kai ne darakta, da an kawo maka fim, kai ne ka yi wannan, kai ne ka yi wancan, kai ne ka yi wancan. A’a, ana so darakta ya zama mai ɗanɗano, wato ya zama mai taste.

“In an kawo ka zaɓa, ka ga wanne za ka yi, wanne za ka bari, wanda ba ka yin da ma ka taɓa yin sa ko kuma ba zai ƙara ma komai ba, ko kuma mashiryin sa bai shirya ba.

“Wannan ne ya sa na ce an daina yin fim barkatai domin yin fim barkatai a wannan tsari na zuwan manyan manhajoji kamar Netflix da Prime, su ba za su karɓi barkatai ɗin ba, domin ba ka tsaya ka yi tunani ba.

“Fim ba a yin sa da yawa, sai an yi tunani an tsamo daga cikin labarurruka, an ba shi kulawa, an so labarin, an yi bincike, sannan ake ɗauka.

“Don haka bayan ka yi wannan mai nagarta kamar guda huɗu ko biyar a shekara ba, ƙarƙari ka yin fim guda biyu a matsayin darakta, har da mai shiryawar.

“Wannan abin farin ciki ne sosai. Don haka fim ba ƙwadago ba ne, ba ɗinkin hula ba ne ko ɗinkin kayan sawa da kai za ka zauna ka ɗinka.

“Abu ne na fiƙira, ɗaukar lokaci da bincike da nazari. Shi ya sa nake cewa fim sai mai zurfin tunani, ba kawai himma ake buƙata ba, zurfin tunani ta yadda za ka ba da labari mai ƙarfi, wanda zai ja hankalin duniya, ba ka ba wa kan ka labarin da da ma shi ka saba ba wa masu kallon ka ba, kuma kun san labarin.

“Ka ba da labarin da duniya za ta kalla, mai kallon ka zai san ka sauya, tunda har ta zama al’ada sukar mu a matsayin ‘yan Kannywood, cewar kullum labari iri ɗaya, har ya zama haka ake kallon mu.

“So, labari mai ƙarfi, wanda ya ke da salon burgewa a kowane minti goma sha biyar, ɗan kallo ya riƙa zabura ya na tunanin me zai faru gaba. Shi ne ake ce wa ‘suspense’ – wani labari wanda za a miƙe tsaye ana tafi in a sinima ne, in kuma a gida ne a maimaita kallo, shi ne ake cewa ‘feed value’, ka yi fim wanda za a maimaita kallon sa ko abokai sun zo ko ‘yan’uwa sun zo a kunna masu shi su kalla.

Malam Kamal Alƙali

“Waɗannan su ne ƙa’idojin irin finafinan da su ke hawa kan wannan manhaja. Ba finafinai ba ne waɗanda aka saba yi ba, wanda daga an yi ‘typing’ mutum ɗaya ya je ya rubuta labari, darakta zai karɓa ya tafi ya yi shutin, a gama a yi ta talla a YouTube. Ba irin waɗannan ba ne gaskiya.

“Wannan ne ya sa ba na da-na-sanin ja baya da na yi, a kan yawan a yi ta gani na ina fim, ko na mutane ko nawa.

“Babban misali, akwai fim ɗin da na yi a cikin shekarar 2020, bayan korona da kaɗan ko kuma kafin ta. Labarin na wani yaro ne da ya samu buguwa a ƙwaƙwalwar sa. Matsalar da ya samu a ƙwaƙwalwar shi ne, tunani da ya ke yi shi muke nuna wa mutane, don haka ba abin da ba zai iya faruwa ba, a ce mutum ya samu taɓin hankali, to ƙwaƙwalwar tasa ka ke kallo, ita kake nuna wa mutane. Sunan fim ɗin ‘Fati’. Umar M. Shareef ne a ciki.

“So, irin waɗannan labarurrukan da ba gama-gari ba, irin su ake buƙata. Shi ya sa ni ba na da-na-sanin ja da baya da na yi, domin gaskiyar magana fim abu ne mai wahala.

“Sannan a yanzu akwai ɗumamar yanayi da ake fama da ita a duniya, ta yadda za ka fito ka yi aiki a cikin zafin rana, domin shi fim ya fi ƙwadago ko kuma dako ma, domin shi ka na amfani ne da ƙwaƙwalwar ka, kuma wannan zafi da ake ciki, ka fito ka yi fim kwana hamsin, wata biyu a rana ku na aiki, abu ne mai gajiyawa.

“Kuma a yanayin ƙasar mu da yanayin tattalin arzikin mu, wanda da ruwan ciki ake jan na rijiya, duk sai kun gaji kun fita daga hayyacin ku.

“Sannan na duba na ga na taɓa yin irin sa? Shi wannan ɗin in ban yi irin sa ba me zai ƙara min a darajar suna da tun tuni an san sunan ka.

“To, wannan dalilin ne ya sa na ja da baya. Waɗannan ginshiƙai biyu, cewar wahalar sa, menene amfanin sa idan na yi, wancan ma na yi, wancan ma na yi? Ko don lafiyar jikin mutum, mutum ma ya taƙaita.

“Da wannan na ke sanar da mujallar Fim, duk da dai kun kasance masu bincike ne, cewar Netflix ta ware dala miliyan talatin domin ‘content’ ɗin Hausa na arewacin Nijeriya.

“Sannan ba sai mutum ya yi fim mai dogon zango har sha uku ba, ana yin biyar, wato ‘limited film’, ana yin shida, ana yin huɗu ma, ta yadda za ka yi labarin ka ba sai ka faɗaɗa shi ba, in ba mai faɗi ba ne.”

Kamal ya yi magana a kan wani guruf da su Rahama Sadau da Abdul Amart su ka buɗe, inda ya ce, “Sai wani guruf na wasu daga cikin ƙwararru masu shirya finafinai na Kannywood da su ka buɗe, su ka yi wata ƙwarya-ƙwaryar guruf. Na san da kyakkyawar niyya su ka yi, domin kada abin ya zama na kowa da kowa, kamar yadda ake ƙorafin kowa darakta da ƙananan finafinai da su ka yi wa Kannywood katutu.

“Sun buɗe wannan guruf da kyakkyawar niyya, sun zaɓo wasu daga cikin ƙwararrun masu shirya finafinai waɗanda su ke da tarihi sun buɗe shi.

“Kawai jan hankalin da zan yi a gare su shi ne, kusan Rahama Sadau ce ta ke jan ragamar guruf ɗin; ita ta sa aka buɗe shi; bin da zan ja hankalin su a kai shi ne, kada ya zama sun yi wa abin ƙyaure sun rufe shi ruf. Domin ita fiƙira, aka ce ‘think outside the box’ – ka yi tunani fiye da iya inda ka ke.

“Sun yi shi don a killace, a waro wasu waɗanda su ka iya fim a ciki, to amma akwai waɗanda su ke a waje waɗanda za a iya tsinto baiwar su a bunƙasa ta.

“Domin ni a ra’ayi na, babu wata ‘idea’ wanda ta ke ba ta da kyau, sai dai in ba a zauna an yi mata fashin baƙi an fito da abin da mai ‘idea’ ɗin ya ke so ya bayyana ba.”

Daraktan ya ba su shawara da cewa, “Don haka ƙofar tasu ta zama mai makulli ce wadda za su iya buɗewa, domin kada su katange kan su ko kuma su jawo abin da zai zama ce-ce-ku-ce duk da ba a rasa shi ga waɗannan wanda su ka gaza. Su yi tunani matuƙa su ƙara faɗaɗa abin, sai su ga damarmakin sun ƙaru.

“A ƙarshe, ina yi mana fatan alkhairi da zuwan wannan wata mai alfarma.

“Sannan ina da albishir na mashahurin fim ɗin da za mu kai shi wannan manhaja, wanda kafin manhajar ta yi wannan albishir, mu mu ka yi wannan ‘standard’ ɗin, wanda mu ka yi shi a kan lungu da saƙon Kano da wasu matsaloli na ƙwacen waya tare da harkar daba, da asalin dalilin da ke sa su shiga harkar daba ɗin.

“Sai mu ka duba zahiri na abin da ke faruwa a birnin ƙwaryar Kano kusa da gidan Sarki. Sunan fim ɗin ‘Wata Rana A Kano’.

“Kuma yanzu akwai shirye-shirye da su ka zo, a hankali mu na shirya su. Shi fim ba abin a yi shi barkatai ba ne.”

Loading

Tags: Kamal AlƙaliNetflix
Previous Post

Mahaifin marubuciya Zuwairiyyah Adamu Girei ya rasu

Next Post

Cewar Minista Idris: Tinubu na kan aikin rage matsalolin Nijeriya 

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Cewar Minista Idris: Tinubu na kan aikin rage matsalolin Nijeriya 

Cewar Minista Idris: Tinubu na kan aikin rage matsalolin Nijeriya 

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!