WATA ƙungiya mai suna ‘Arewa Forum’ za yi taron saukar Alƙur’ani tare da yin addu’o’i don tunawa da jarumar Kannywood marigayiya Hajiya Zainab Musa Booth da sauran ‘yan fim da su ka rasu.
Za a yi taron da misalin ƙarfe 3:00 na yamma a ranar Juma’a mai zuwa a Social Welfare da ke Court Road, Kano.

A katin gayyatar da aka wallafa, an nuna cewa za ƙungiyar za ta shirya taron ne tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), reshen Jihar Kano, da Kannywood Elders Forum.
Mashirya taron sun ce su na gayyatar ‘yan Kannywood domin halartar taron.
Mujallar Fim ta ruwaito cewar Hajiya Zainab Booth ta rasu ne a Kano a ranar Alhamis, 1 ga Yuli, 2021 sakamakon tiyata da aka yi mata a ƙwaƙwalwa.
Mutuwar ta ta girmama masana’antar finafinan Hausa ta Kannywood inda take a matsayin uwa ga ɗimbin ‘yan fim.