• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, June 6, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Za mu taka wa Netflix da ire-iren su burki domin za su iya jawo fitina, cewar Gwamnatin Tarayya

by DAGA IRO MAMMAN
December 3, 2021
in Labarai
1
Shugaban NFVCB, Alhaji Adedayo Thomas, ya na gabatar da jawabi a taron

Shugaban NFVCB, Alhaji Adedayo Thomas, ya na gabatar da jawabi a taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GWAMNATIN Tarayya ta bayyana cewa za ta taka wa kamfonin da ke yaɗa finafinai da waƙoƙi a intanet ko talbijin burki domin za a iya amfanin da su a jawo fitina a Nijeriya.

Ministan Yaɗa Labarai da Kyautata Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, shi ne ya bayyana haka a wajen babban taron da Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa (NFVCB) ta yi da irin waɗannan kamfanonin shekaranjiya a Legas.

Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba ku labari a ranar 28 ga Nuwamba, 2021 cewa ana kiran shirye-shiryen da waɗannan kamfanonin ke yaɗawa ta hanyar intanet ko talbijin da‘OTT’ (wato ‘over-the-top content’).

Sun haɗa da finafinai, waƙoƙi ko shirye-shiryen talbijin, kuma kamfanonin na tura wa mai buƙata ta hanyar intanet ko akwatin talbijin a bisa irin buƙatar sa, kuma zai riƙa biyan kuɗi.

Kamfanonin da ke yaɗa su a Nijeriya sun haɗa da Netflix, Amazon, Showmax, Africa Magic, YouTube, Northflix, Iroko TV da ire-iren su.

A jawabin da ya gabatar a wajen buɗe taron na kwana biyu ne minista Lai ya faɗi matsayin gwamnati a kan shirye-shiryen, inda ya yi nuni da cewa kamfanonin da ke yaɗa su sun ƙara samun farin jini da karɓuwa ga jama’ar Nijeriya tun daga lokacin zaman dole da annobar korona (COVID-19) ta jawo, “shi ya sa za a ɗora su a bisa turbar doka.” 

Wani sashe na mahalartan taron

Ministan, wanda Daraktar Yaɗa Labarai da Kimiyya a ma’aikatar sa, Madam Comfort Ajiboye, ta wakilta, ya yi nuni da cewa za a iya amfani da kamfanonin “a jawo fitina” kuma a yi wa tsarin dimokiraɗiyyar Nijeriya zagon ƙasa.

Tun da fari sai da Babban Darakta kuma Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa, Alhaji Adedayo Thomas, ya gabatar da jawabin buɗe taron, inda ya bayyana cewa an kira taron ne domin a yi musayar ra’ayi kan yadda za a fito da sababbin manufofi da tsare-tsare a gwamnatance waɗanda za su yi aiki a kan masu yaɗa shirye-shirye ta hanyar yanar gizo ko talbijin a Nijeriya.

Ya ce, “Da yake waɗannan shirye-shirye su na isa ga sama da kashi 50 cikin ɗari na al’ummar mu, ya zama wajibi mu kira wannan taron inda za a tattaro masu ruwa da tsaki da masu tsara dokoki domin su tattauna saboda a fito da bayyanannun tsare-tsare kan ɗora masu yaɗa shirye-shirye a intanet da talbijin da kuma masu ƙirƙirar shirye-shiryen bisa turbar doka.” 

Shugaban ya ce kamfanonin yaɗa shirye-shiryen sun kasa kimtsa kan su da kan su domin bin doka, wanda hakan ne ya jawo har ake tattaunawa a kan su a yau.

Thomas ya sha alwashin cewa, “Ba burin fito da wannan doka ba ne ya takure fasaha, amma dai ana so ne a daidaita sahu tare da inganta gasa mai tsafta don cigaban al’umma da tattalin arziki.” 

A taron, jami’an gwamnati da na kamfanonin yaɗa shirye-shirye a intanet da talbijin da sauran masu ruwa da tsari a al’amarin, irin su ‘yan fim, sun tattauna kan jigon taron, wato “Al’amuran Dokokin Tace Finafinai na Nijeriya da Tsarin Kawo Gyara Ga Kamfanonin Yaɗa Finafinai da Bidiyo da Masu Ƙirƙirar Shirye-shiryen Kallo,” wato a Turance, “Implications of Nigerian Censorship Laws and Regulatory Framework for OTT Streaming Services and Content Providers”.

Daraktan Kula da Tsare-tsaren Jama’a na kamfanin Netflix mai kula da yammacin Afrika, Shola Sanni, na ɗaya daga cikin mahalarta taron.

Wasu mahalartan taron

Mujallar Fim ta fahimci cewa tsohon shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), wadda ita ce uwar ƙungiyoyin masu harkar finafinan Hausa, Dakta Ahmad Sarari, kusam shi kaɗai sanannen ɗan fim da ya halarci taron daga Kannywood. 
 Akwai kuma membobin ƙungiyoyi daban-daban na masana’antar shirya finafinai ta Nollywood waɗanda su ka haɗa da ƙungiyar jarumai (AGN) da ta daraktocin fim (DGN) da na mamallaka gidajen sinima da sauran su sun halarci taron.

Haka kuma akwai wakilan kamfanonin yaɗa shirye-shirye a intanet na cikin gida da na ƙasashen waje, da na gidajen talbijin masu amfani da satalayit, da kuma masu ƙirƙirar shirye-shirye waɗanda da Turanci ake kira ‘content creators’.

An yi taron a otal ɗin ‘Radisson Hotel’ da ke unguwar Ikeja GRA a Legas a ranakun 1 da 2 ga Disamba, 2021.

Alhaji Adedayo Thomas (a tsakiya) tare da daraktocin Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa
Dakta Ahmad Sarari (na 3 daga dama) tare da shugabanni a wajen taron
Ɗaya daga cikin mahalarta ta na gabatar da jawabi. Hotuna daga: NFVCB

Loading

Tags: adedayo thomasAhmad SararicensorshipComfort Ajiboyehausa filmsKannywoodLai MohammedMOPPANNational Film and Videos Censors BoardNetflixNFVCBNorthflixOTTOver the Top contentShola Sanniwakokin HausaYouTube
Previous Post

Jaruma Maryam Waziri da ɗan ƙwallo Tijjani Babangida sun angwance

Next Post

Tunawa da Yaƙin Basasar Kano na 1894

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post
Sarkin Kano Alu Babba (Maisango) bayan Turawa sun kwaɓe shi daga gadon sarauta

Tunawa da Yaƙin Basasar Kano na 1894

Comments 1

  1. Jamila Adamu Yaro says:
    3 years ago

    Ai yan kannywood babu kishin masana’antar a ran su, domin mafi yawan su neman kudi ne yasa suke cikin ta. Shiyasa za ayi ta tarurruka amma ace mutum daya ne a cikin su zai halarta, wani sa’in ma babu ko mutum guda, kaico!!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!