SABON shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Arewa (Arewa Film Makers Association of Nigeria, AFMAN), Alhaji Sani Sule Katsina, ya bayyana cewa babban ƙudirin da ke gaban sa shi ne tsarkake masana’antar finafinai ta Kannywood, kuma gyaran zai fara ne daga su kan su shugabannin harkar.
Ya ce, “Za mu tsarkake kan mu, mu tsarkake tafiyar gaba ɗaya don a samu tsafta a cikin ta in Allah ya yarda.”
An zaɓi Sani Katsina ɗin ne a wajen babban taron ƙungiyar na ƙasa, karon farko, wanda aka gudanar a Kano a yammacin ranar Lahadi, 23 ga Janairu, 2022.
A taron, an zaɓi shugabannin a muƙamai 16 da za su jagoranci ƙungiyar wadda ta haɗa jihohin Arewa 19.

Bayan an kammala taron haɗi da gudanar da zaɓuɓɓuka, kwamitin shirya zaɓen, a ƙarƙashin jagorancin Mika’ilu Isa bin Hassan (Gidigo), ya gabatar da sakamakon abin da su ka tattara na zaɓen inda aka sanar da cewa Alhaji Sani Sule Katsina ne aka zaɓa a matsayin shugaban ƙungiyar.
Shugabannin da aka zaɓa ɗin dai su ne:
1. Sani Sule Katsina – Shugaba
2. Rasheeda Adamu Maisa’a daga Jihar Kano – Mataimakiyar Shugaba ta 1
3. Wassh Waziri Hong daga Kaduna – Mataimakin Shugaba na 2
4. Habibu Baffa Jalingo daga Taraba – Mataimakin Shugaba na 3
5. Salisu Muhammad Officer daga Kano – Babban Sakatare
6. Kwamared M.B. Mukhtar daga Neja – Ma’aji
7. Jamilu Ahmad Yakasai daga Kano – Sakataren Kuɗi
8. Amina Adamu daga Kano – Mataimakiyar Sakatare
9. Nasiru B.A. Hassan daga Sokoto – Sakataren Tsare-tsare
10. Audu Boda daga Katsina – Mataimakin Sakataren Kuɗi
11. Muhammad Mukhtar Daneji daga Kano – Jami’in Hulɗa da Jama’a na 1
12. Yahaya B. Abubakar daga Kebbi – Jami’in Hulɗa da Jama’a na 2
13. Jamila Umar Nagudu daga Bauchi – Mataimakiyar Sakataren Tsare-tsare
14. Hadizan Saima daga Kano – Jami’ar Walwala
15. Hamza Jibrin – Mai Binciken Kuɗi na 1
16. Halima Muhammad – Mai Binciken Kuɗi ta 2

Jim ƙaɗan bayan kammala karɓar rantsuwar kama aiki ne sabon shugaban ƙungiyar ya yi wa mujallar Fim ƙarin haske kan wannan nauyi da aka ɗora masa inda ya fara da gode wa Allah tare da faɗin, ”Na yi matuƙar farin ciki da wannan nauyi da Allah ya ɗora mani kuma ina roƙon Ubangiji Allah ya ba ni damar da zan sauke kuma in yi abin da ya kamata da mutanen da su ka dace.”
Alhaji Sani ya kuma bayyana ƙudirin da ya ke son cimmawa a wannan ƙungiya domin samun cigaba ta kowane fanni, ya ce: “Akwai ƙudire-ƙudire saboda na san matsalolin da ke cikin wannan masana’anta gaba ɗaya tunda na daɗe a cikin ta kuma ina shugabanci a cikin ta kuma na san yadda za mu fuskance su.
“Ɗaya daga cikin matsalolin mu shi ne rashin ƙofa ta shigowa da ta fita kuma da rashin katanga inda wasu sai su yi wani abu ake zaton mu ne. To in Allah ya yarda za mu yi abin da za mu gyara kuma za mu ba wa jama’a mamaki.
“Za mu tsarkake kan mu, mu tsarkake tafiyar gaba ɗaya don a samu tsafta a cikin ta in Allah ya yarda.”
Haka kuma ya ce maganar ƙalubale da man ya riga ya san da su kuma sun shirya tsaf don ganin an fuskance su tare da kawo ƙarshen su.

Taron dai ya samu halartar wasu daga cikin dattawan Kannywood, tare da shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah).