INNA lillahi wa inna ilaihir raji’un! Allah ya yi wa ɗaya daga cikin jarumai mata iyaye a Kannywood, Hajiya Zainab Musa Booth, rasuwa.
Wata ƙwaƙƙwarar majiya ta faɗa wa mujallar Fim cewa ta rasu ne ɗazu a Kano sakamakon tiyatar ƙwaƙwalwa da aka yi mata.
Gobe Juma’a, 2 ga Yuli, 2021, da ƙarfe 8 na safe za a yi jana’izar ta a gidan ta da ke kallon Asibitin Premier a Court Road, Kano.
Hajiya Zainab ita ce mahaifiyar jaruman fim guda uku, wato Sadiya matar jarumi kuma mawaƙi Yakubu Muhammad a da, da ƙannen ta biyu, Amude Booth da Maryam Booth.
Saƙo na ƙarshe da aka ga marigayiyar ta tura a soshiyal midiya shi ne wani bidiyo da ta yi a cikin mota a ranar 16 ga Disamba, 2020 inda ta ke tabbatar wa da mutane cewa cutar korona (Covid-19) fa da gaske ce, saboda haka kada su yi wasa da ita.

A watan Maris, ɗiyar ta, fitacciyar jaruma Maryam Booth, ta sanar da jama’a cewa za a yi wa mahaifiyar ta aiki a ƙwaƙwalwar ta kuma ta buƙaci jama’a da su taya ta da addu’a.
‘Yan fim sun girgiza da wannan babban rashi da aka yi na jarumar da da yawan su su ke kira da Mama, kuma sun yi addu’ar Allah ya rahamshe ta.
Wasu kuma sun yi wa ‘ya’yan ta gaisuwa.
Allah ya jiƙan ta, ya sa bakin wahalar kenan, amin.