• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Ƙungiyar Alƙalam za ta yi taron tunawa da marubuci kuma ɗan jarida marigayi Mahmoon Baba-Ahmed

by DAGA WAKILIN MU
February 2, 2023
in Marubuta
0
Marigayi Alhaji Mahmoon Baba-Ahmed

Marigayi Alhaji Mahmoon Baba-Ahmed

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƘUNGIYAR Marubuta Alƙalam da ke Kaduna ta bayyana cewa za ta shirya taron tunawa da uban ƙungiyar kuma gwarzon ɗan kishin ƙasa ɗin nan, Alhaji Mahmoon Baba-Ahmed, wanda Allah ya yi wa rasuwa shekaru biyar da su ka gabata.

Shugabar ƙungiyar, Hajiya Halima Abdullahi K/Mashi, ta bayyana a cikin wata takarda ga manema labarai cewa za a yi taron a Gidan Arewa da ke Kaduna a ranar Alhamis, 9 ga Fabrairu, 2023, wadda ta yi daidai da shekaru biyar cur da rasuwar marubucin.

Alhaji Mahmoon ya rasu ne a Kaduna a ranar Alhamis, 9 ga Fabrairu, 2018, ya na da shekaru 77 a duniya.

Mahmoon Baba-Ahmed sanannen ɗan jarida ne kuma marubuci wanda ya yi fice a aikin rediyo a matsayin wakilin gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna a jihohi da dama. Daga bisani ya riƙe muƙamai da su ka haɗa da Shugaban gidan Rediyon Kano da Manajan Daraktan Hukumar Yaɗa Labarai ta Jihar Kaduna (KSMC).

Haka kuma ya kasance mai sharhi kan al’amurran yau da kullum a filayen musamman da aka ware masa a jaridu da su ka haɗa da Triumph, Blueprint da Aminiya, da kuma gidajen talabijin na DITV da Liberty da gidan rediyo na Alheri da na Liberty.

Marigayi Mahmoon ya rubuta littattafan adabi guda shida a rayuwar sa waɗanda su ka haɗa da littafin waƙe mai suna ‘Ɗan Hausa’, da littattafan wasan kwaikwayo guda biyu (‘Uwani Reza’ da ”Yar Halas’), da fassarar littattafai uku na mashahurin marubucin nan na ƙasar Ingila, wato William Shakespeare.

Littattafan Shakespeare da ya fassara su ne: ‘Macbeth’ (‘Makau’), ‘Julius Caesar’ (‘Jarmai Ziza’), da ‘Romeo and Juliet’ (‘Habiba Ta Habibu’). 

Takardar sanarwar ta ce ɗaya daga cikin abubuwan ban-sha’awa da za a gudanar a taron shi ne gabatar da littafin ƙarshe da Mahmoon ya rubuta, wato ‘Habiba Ta Habibu’, wanda shi kaɗai ne marigayin bai samu bugawa ba har ya rasu, amma an buga shi a bana.

Hajiya Halima ta kuma bayyana cewa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, shi ne babban baƙo na musamman a taron, yayin da Shugaban gidan talabijin da rediyo na Liberty, Dakta Ahmed Tijjani Ramalan, shi ne shugaban taron.

Bugu da ƙari, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, zai kasance uban taron, yayin da tsohon Shugaban Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya, Mai Shari’a Umaru Abdullahi (Walin Hausa), shi ne babban baƙo na musamman.

Ta ce Shugaban Shiyyar Kaduna ta hukumar Gidan Rediyon Tarayyar Nijeriya (FRCN), Alhaji Buhari Auwalu, shi ne babban baƙo mai jawabi, sannan babban malami a Jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Adamu Ibrahim Malumfashi, zai yi sharhi kan littattafan marigayin.

A cewar shugabar ƙungiyar, manufar taron ita ce a tuno da muhimman ayyukan kishin ƙasa da Alhaji Mahmoon yayi, tare da ƙara kwaɗaita wa jama’a muhimmancin sambarka ga magabatan mu da su ka ba da gudunmawa ga cigaban ƙasa ta hanyoyin da Allah hore masu.

Ta ce za kuma a yi amfani da wannan damar a karrama wasu ‘ya’yan ƙungiyar ta Alƙalam waɗanda su ka riga mu gidan gaskiya.

Loading

Tags: Arewa HouseDITV Alheriɗan jaridaFRCNgabatar da littafiHalima Abdullahi K/MashiƘungiyar AlƙalamLiberty TalbijinMahmoon Baba-Ahmedmarigayimarubucin HausaShakespearetaron tunawa
Previous Post

Kotu ta tura Murja Ibrahim Kunya gidan yari

Next Post

Yau za a fara shagulgulan bikin auren darakta Aminu Al-Rahuz

Related Posts

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro
Marubuta

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro

January 10, 2026
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama
Marubuta

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama

December 25, 2025
‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa
Marubuta

‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa

December 25, 2025
Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo
Marubuta

Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo

December 24, 2025
Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu
Marubuta

Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu

December 19, 2025
Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata
Marubuta

Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata

December 8, 2025
Next Post
Ango Aminu Al-Rahuz da amarya Bilkisu Muhammad Bello

Yau za a fara shagulgulan bikin auren darakta Aminu Al-Rahuz

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!