• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, October 8, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Haramcin waƙa ta: Na yi gum, ba zan ce komai ba yanzu, inji Gwanja

by DAGA ABBA MUHAMMAD
September 8, 2022
in Labarai
0
Ado Gwanja

Ado Gwanja

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCEN mawaƙi Ado Isa Gwanja ya ce a halin yanzu babu abin da za a ji daga bakin sa a kan abubuwan da su ke faruwa da shi game da waƙoƙin sa.

Gwanja ya yi wannan taƙaitaccen bayanin ne a lokacin da mujallar Fim ta tuntuɓe shi a kan haramta waƙar sa ta ‘Warr’ a gidajen rediyo da talbijin da Hukumar Kula Da Gidajen Rediyo da Talbijin ta Nijeriya (NBC) ta yi da kuma ƙarar da wasu lauyoyi su ka kai shi a kotu a kan waƙoƙin sa.

Gwanja faɗa wa mujallar Fim cewa, “Yanzu kam ba abin da za a ji daga baki na. Kawai na yi shiru kawai. Ba zan kuma magana ba, saboda ina so in jira in ji.”

A ci-gaba da ce-ce-ku-cen da ake ta yi a game da matakin da NBC ta ɗauka a kan waƙar, wasu na ganin ai an kashe maciji ne ba a sare kan sa ba.

Dalili kuwa shi ne kusan dukkan al’ummar wannan zamani a yanzu sun koma mu’amala da soshiyal midiya ne.

A halin yanzu a kafafen sada zumunci na zamani, duk inda ka leƙa za ka ga zancen Ado Gwanja kawai ake yi, kuma kowa da irin abin da ya ke faɗi. Yawancin jama’a su na nuna rashin jin daɗin su game da haramta waƙar da hukumar ta yi.

Ɗaya daga cikin mutanen da su ka yi rubutu a shafukan su na soshoyal midiya a kan maganar shi ne Rabi’u Biyora, wani ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa mazaunin Jihar Kano, inda ya ce, “A yau da na ga wata sanarwa da hukumar NBC da ke Nijeriya ta fitar a kan waƙar mawaki Ado Gwanja. Sai nan da nan tunani na ya koma kan wata waƙa da ita ma hukumar ‘yan sandan Amurka ta taɓa haramta sauraren ta a gaba ɗaya a ƙasar ta Amurka a shekarar 1988.

“Mawaƙan ƙungiyar ‘Niggas With Attitudes’ (NWA), Ice Cube, Easy-E, Arabian Prince, Dr. Dre,  DJ Yella, da kuma MC Ren, su ne su ka fitar da wata waƙa a ranar 9 ga watan Agusta na shekarar 1988, sakamakon cin zarafin da ‘yan sanda su ka yi musu a kan hanyar su ta zuwa situdiyo a garin Compton da ke birnin California, sai su ka rubuta waƙa mai sunan ‘Fuck the Police’, a cikin waƙar su ka yi bayani a kan halayyar cin zarafin baƙaƙen mutane da ‘yan sandan Amurka ke yi.

“Lokacin da su ka fitar da waƙar, mutanen da ke sauraren ta ba su shige iya birnin California ba, sai ‘yan wasu jihohin da ba su shige biyu ba. Kwatsam, sai hukumar ‘yan sandan FBI ta Amurka ta fitar da sanarwa a hukumance a kan haramta sauraren waƙar gaba ɗaya, amma kuma hakan da su ka yi sai ya zama kamar fetur su ka yayyafa wa wuta dangane da waƙar; labarin waƙar ya fantsama a duk ƙasar Amurka, ya kasance kusan dukkan matasa su ka koma neman waƙar da sauraren ta, har hakan ya ƙara haifar da wasu tarin mawaƙan da ba a ƙasar Amurka su ke ba.

“Kafin yau da hukumar NBC su ka haramta waƙar Ado Gwanja, mafi yawan matasan da ke kudancin Nijeriya ba su ma san da waƙar ‘Warr’ ba, amma idan ba a yi sa’a ba, wannan dakatarwar za ta iya zama kamar talla ne aka yi wa Ado Gwanja a kan waƙar da kuma sauran waƙoƙin sa, domin dai ba mamaki labarin dakatarwar ya fito a gidan talabijin na tarayya da sauran manya-manyan kafafen yaɗa labarai na Nijeriya.

“To, Allah dai ya kyauta.”

Loading

Tags: Ado GwanjaAmurkaChassharamciNBCRabi'u BiyoraRabi'u Biyora.waƙaWarr
Previous Post

Dattawan Kannywood sun yi na’am da ƙarar da Iyan-Tama ya kai mai ɓata sunan ‘yan fim

Next Post

Batun Gwanja: In gaskiya ne, NBC ta soke soshiyal midiya mana – mawaƙi Ɗayyab Maiɗa’a

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
Ɗayyab Hassan (Maiɗa'a)

Batun Gwanja: In gaskiya ne, NBC ta soke soshiyal midiya mana - mawaƙi Ɗayyab Maiɗa'a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!