BABBAN furodusan Kannywood Usman Mu’azu ya yi wa ‘yar aminin sa, mawaƙin nan marigayi Alhaji Isyaku Muhammad Forest, da angon ta fatan zaman lafiya mai ɗorewa a auren da su ka yi.
Furodusan ya yi wannan addu’a ne tare da ɗora wasu hotunan amarya A’isha Isyaku Forest (Amira) tare da aminan mahaifin ta a Instagram.
Alhaji Usman ya ce: “Bayan ɗaurin auren ‘yar mu, ‘yar marigayi Isyaku Forest, Allah ya jiƙan shi, amin, wanda aka yi ranar Lahadi, 11-9-2022, Amira da mijin ta Habeeb, Allah ya ba su zaman lafiya mai ɗorewa.”

Hoton farko na jarumin barkwanci Baban Chinedu ne tare da A’isha, haka hoto na biyu, mawaƙi Ikram Kano ne tare da ita, sai kuma hoto na uku, Usman Mu’azu ne tare da ita.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa waɗannan mutane sun jajirce wurin riƙe amanar da ke tsakanin su da marigayin, domin su ne waɗanda su ka tsaya, tsayin daka, don ganin an yi auren cikin nasara da kuma kare dukkan abubuwan da marigayin ya ke so da wanda ba ya so.
A yau Laraba ne, 21 ga Satumba, 2022 Usman Mu’azu ya yi rubutun, bayan kwana goma da ɗaura auren.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, Amin.

![]()






