TUN da ake ba a taɓa samun mutanen da su ka jawo wa Kannywood abin faɗa kamar Naziru Ahmad (Sarkin Waƙa) da Ali Artwork da Mustapha Nabraska ba, a cewar jarumi a Kannywood, Iliyasu Abdulmumi (Tantiri).
Ya ce ‘yan fim da ke sauya sheƙa zuwa rundunar Kwankwasiyya bayan faɗuwa a zaɓen gwamnan Jihar Kano mutane ne da ba su san mutuncin kan su ba kuma makwaɗaita ne.
Tantiri, wanda kuma darakta ne kuma furodusa, ya faɗi haka ne a lokacin tattaunawar sa da mujallar Fim dangane da yadda wasu ‘yan fim su ke barin gwamnatin Ganduje da ta faɗi a zaɓen zuwa sabuwar gwamnati mai jiran gado ta Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Ya ce: “Su waɗannan ‘yan fim ɗin da su ke yin tururuwa zuwa sabuwar gwamnati, mutane ne da ba su san mutuncin kan su ba, kuma sun zubar da ƙimar su da ta masana’antar Kannywood, domin kowa zai rinƙa kallon ‘yan fim a matsayin marasa daraja.”
Ya ce in ban da rashin tunani ya za a yi ka shafe shekaru ka na adawa da mutane, kuma lokaci guda don sun ci zaɓe ka koma cikin su wai ka na tare da su? “Ai wannan ba ka saya wa kan ka da sana’ar ka mutunci ba. Kuma su waɗannan da ka koma cikin su ka na ganin za su yarda da kai? Wannan ai rashin sanin darajar kai ne kuma zubar da mutuncin masana’antar Kannywood, domin za a rinƙa ɗaukar ‘yan fim kamar wasu karuwai, kawai mai ba su kuɗi su ke bi.”
Ya ƙara da cewa: “Maganar gaskiya, ba a taɓa samun mutanen da su ka jawo wa masana’antar Kannywood abin faɗa kamar Naziru Sarkin Waƙa da Ali Artwork da Mustapha Nabraska ba, domin idan ka duba daga bara zuwa bana waɗannan mutane sun jawo wa masana’antar Kannywood zagi da cin mutunci don haka tun da na ke ban taɓa yin da-na-sanin kasancewa ɗan fim ba sai daga bara zuwa bana, saboda zubar da mutuncin da mutanen nan su ka jawo wa masana’antar, kuma dai su ne babu kunya su ka koma jam’iyyar da ta ci zaɓe.
“Kuma na san ba za su taɓa yarda da su ba. An gane su makwaɗaita ne, ba sa zama a jam’iyyar da ba ta da mulki, saboda ba su da sana’a sai yawon maula.
“To ni kuma ina da sana’a yanzu tun da an gama siyasa zan koma sana’a ta, su kuma da ba su da sana’a kuma su na da kwaɗayi sai su je su yi ta yawon zubar da mutunci. Amma ni dai ba zan je wajen da zan zubar da mutunci na ba.”
![]()






