JARUMI kuma mawaƙi a Kannywood, Adam A. Zango, ya bayyana cewa ba zai sake yin aure ba har abada idan har ya saki matar sa da su ke rigima yanzu, wato Safiyya Umar Chalawa.
Ya faɗi haka ne a cikin wani guntun bidiyo da ya ɗauka kuma ya wallafa shi a TikTok a yau. Ya yanke wannan shawara ne saboda aure-aure ya ishe shi.
A bidiyon mai tsawon minti uku, an ga jarumin zaune a cikin motar sa, ya na magana a cikin alhini kamar zai yi kuka, ya na ba da labarin yadda Safiyya ta ƙi bin umurnin sa na ta daina kasuwanci a intanet da ta ke yi.
Ya nuna cewa matar tasa ta samu ɗaurin gindin iyayen ta kan wannan al’amari, ya ce tunda haka ne kuwa to kwanan nan “za a ji labari mara daɗi” idan har ba a daidaita ba.
Zango ya ce: “Tunda sun zaɓi kasuwancin da ta ke yi fiye da zaman auren ta, ba ni da zaɓi. A kowanne lokaci daga yanzu, za a ji labari mara daɗi. A gafarce ni, wannan shi ne.

“Saboda ina sananne ba zan kashe kai na saboda mabiya na ko masoya na in birge su ba in ci gaba da zama da baƙin ciki saboda babu yadda na iya.”
Ya ci gaba da cewa, “Billahil lazi la ila ha illa huwa, har zuciya ta da na ke maganar nan ba so na ke ba, amma ba ni da zaɓi. To, in Allah ya sa an daidaita, ya yi kyau, idan ba a daidaita ba Allah zai yanke. Babu abin da ya fi ƙarfin addu’a.
“Na san dai aure ana yin shi ne saboda raya sunnar Manzon Allah s.a.w.), a kuma tara zuri’a da sauran su. Ina da zuri’a, ina da ‘ya’ya, don haka ba ni na yi kai na ba kuma ba na cire rai da rahamar Allah.
“Amma ina ganin na gama aure. Da izinin Allah na gama aure, kuma ina roƙon Allah ya kare ni daga dukkanin abubuwan da na ke gujewa ya sa na ke ta yin wannan auren.
“Daga na rabu da mace in sake yin wani auren, wanda in mutum ya zama maɗaukaki, zai dinga ganin irin waɗannan abubuwan da za su dinga bin shi. Idan mutum ba imani ne da shi ba ko kuma addu’a da dauriya, sai ya kauce hanya.
“Kada mutum ya koma ya dinga bin ‘yan mata da sauran su, wanda hakan ya sa ina rabuwa da mace na ke sake yin auren saboda in kauce wa wannan hanyar.”
Mujallar Fim ta ruwaito cewa an ɗaura auren Zango da Safiyya ne a ranar Juma’a, 26 ga Afrilu, a 2019 a masallacin fadar Sarkin Gwandu da ke garin Gwandu a Jihar Kebbi.
Sun haifi ‘ya ɗaya mai suna Furaira, amma saboda sunan mahaifiyar sa ne sai ake mata laƙabi Princess Diana. Ita ce ta bakwai a jerin ‘ya’yan sa (huɗu maza, uku mata).
Wannan shi ne auren sa na shida da ya yi, bayan ya saki mata biyar da ya aura a baya ɗaya bayan ɗaya.
A bidiyon da ya yi, Zango ya nuna bai saki Safiyya ba, amma ba ta gidan sa.
Idan har ya sake ta ɗin, to zai ƙara tabbatar da kallon da ake yi masa na mai auren ɗanɗano ko auri-saki duk da gudun wannan kallon da ya ke yi.
