
SANNU a hankali dai ’yan fim sai kara girma ake yi, don kuwa yanzu shagalin biki ya fara komawa na ‘ya’ya ba kamar a lokacin baya ba da su ne su ke shirya wa kan su biki, musamman ma na zagayowar ranar haihuwa.
Samira Ahmad ma ta bi sahun iyayen da su ke shirya wa ’ya’yan su bikin zagayowar ranar haihuwa, domin kuwa a ranar Juma’a, 16 ga Disamba, 2016 ne ita da tsohon maigidan ta, T.Y. Shaban, su ka shirya wa ’yar su, A’isha (Nunu), wani gagarumin biki na tunawa da ranar haihuwar ta, wanda a yanzu ta cika shekaru uku cur kenan.
Taron bikin, wanda aka shirya shi a wajen shakatawar yara na Roxy da ke Titin Ahmadu Bello a cikin garin Kano, ya samu halarta dimbin jama’a, musamman ma yara wadanda aka kai su don su taya ta murna.
An fara bikin da misalin karfe 5 na yamma, aka kai karfe 8 na dare. Yara sun rausaya cikin nishadi yadda su ke so.
Bayan kade-kade da raye-rayen da aka yi, an ci abinci da kuma kayan tsotse-tsotse na yara, sannan aka kai yara bangaren kayan wasanni su ka sha shagalin su.
Cikin wadanda su ka halarci bikin akwai uwargidan Shaba, wato Rukayya, da Rukayya Umar Dawayya, Mansura Isa, Fauziyya Sani (Maikyau) da dai sauran su.
![]()







