• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Matsalar Marubuta: Mun fara gano bakin zaren, inji Rukayya Abdullahi Dangado

by DAGA MUKHTAR YAKUBU A KANO
March 28, 2018
in Marubuta
0
Rukayya Abdullahi Dangado

Rukayya Abdullahi Dangado

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
IDAN ana maganar fitattun marubuta a cikin mata a yanzu, Rukayya Abdullahi D’angado ta na cikin na sahun gaba, musamman idan aka yi la’akari da littattafan da ta rubuta har guda 10. Baya ga haka, marubciyar ta karbu sosai a wajen masu karatu. Don haka ne ma ake rububin littafin ta a duk lokacin da ya fito kasuwa. Ta iya rubutu mai isar da sako cikin hikima ta yadda mai karatu zai kai ga karshen labarin ba tare da ya gundire shi ba. Domin jin ko wacece Rukayya, wakilin mu a Kano ya tattauna da ita, kamar haka:

BAHAUSHIYA: Da farko za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatu.

RUKAYYA DANGADO: To, assalamu alaikum. Ni dai suna na Rukayya Abdullahi Dangado. Ni haififfiyar Kano ce. An haife ni a unguwar Kantudu, Dala, shekaru 29 da su ka wuce. Na yi makarantar firamare da sakandire, daga nan kuma aka yi min aure. A yanzu ina da ’ya’ya uku,  su na nan da ran su. 

BAHAUSHIYA: Ya aka yi ki ka samu kan ki a harkar rubutu?

RUKAYYA DANGADO: Yadda na samu kai na a harkar rubutu shi ne, da farko ni na kasance ina sha’awar karatun littattafai tun kafin na yi aure, amma ban samu damar haka ba saboda karatu da kuma aikin gida. Amma da na yi aure sai na samu lokacin da na ke karanta littafi, kuma sai ya zama karatun littafi bai kawo min matsala da miji na ba.
To a haka ne na ga irin kokarin da marubuta su ke yi na fadakarwa da ilimantarwa. Wannan shi ne ya ja hankali na na fara rubuta littattafai. Ga shi kuma har Allah Ya kawo mu lokacin da ake damawa da mu. 

BAHAUSHIYA: A wacce shekara ki ka fara fitar da littafi?

RUKAYYA DANGADO: Na fara fitar da littafi a 2006; kuma littafi na da ya fara shiga kasuwa a lokacin shi ne ‘’Yar’uwa Ko Kishiya?’

BAHAUSHIYA: Wanne littafi ne ya fito da ke aka san ki a matsayin marubuciya?

RUKAYYA DANGADO: Littafin dai da na fara yi ‘’Yar’uwa Ko Kishiya?’ shi ne ya fito da ni, domin ya samu karbuwa duk da ina sabuwa a lokacin, don haka shi ne ya jawo min daukaka a wajen masu karatu. Na gina labarin ne a kan zamantakewar  uwargida da abokiyar zaman ta da kuma yaran da su ka haifa. To na kawo darasi a kan yadda ya kamata su zauna, da kuma nuna cewar zuwa wajen boka ba ya kawo ci-gaba a rayuwa, a fuskanci gaskiya da rikon amana.

BAHAUSHIYA: Zuwa yanzu littattafan da ki ka yi za su kai kamar nawa?

RUKAYYA DANGADO: A yanzu dai littattafan da na yi sun kai guda  goma, su ne kamar haka: ‘’Yar’uwa Ko Kishiya?’, ‘Menene Matsayi Na?’, ‘Aure Na Jari Na’, ‘Yaya Zan Yi Da Rashin Gata?’, ‘Hudubar Shaidan’, ‘Kuka Ya Zama Dole’, ‘Ban Yi Wa Kai Na Adalci Ba’, ‘Zaluncin Kauna’, ‘Ishara’, ‘Wa Zai So Ni?’

BAHAUSHIYA: Wane littafi ki ka fi so a cikin littattafan ki?

RUKAYYA DANGADO: To, littafin da na fi so a cikin littattafai na shi ne ‘Ishara’. Ina son sa ne ba don komai ba sai yadda salon labarin ya bambanta da sauran wadanda na rubuta, musamman yadda na bata tsawon lokaci har kusan shekara ina rubutun sa, sabanin sauran da ba na daukar lokaci na ke gamawa. Don haka sai salon sa ya zo da jan hankalin mai karatu.

BAHAUSHIYA: Wadanne irin matsaloli ki ke fuskanta a harkar rubutu?

RUKAYYA DANGADO: Matsaloli kam an fuskance su, don ba za a ce babu ba, musamman yadda kasuwar littafin ta ke. Ka san kukan marubuta kullum a kan ’yan kasuwa ne, yadda su ke rike mana kudi, kuma ba wai don ba a sayar ba ne, kawai dai fitowar kudin ce ta ke zama wahala, don kafin su fita sai an kai ruwa rana. Amma dai yanzu mun fara gane bakin zaren wajen dakatar da duk wanda bai biya kudi ba, to ba za mu ba shi kaya ba.

BAHAUSHIYA: Wadanne irin nasarori ki ka samu a harkar littafi?

RUKAYYA DANGADO: Ina godiya ga Allah don na samu nasara ta bangarori daban-daban. Littafi ya kara daga daraja ta fiye da yadda ba na zato. Ina jin dadi a duk lokacin da na ga masoya na masu karatun littafi na.

BAHAUSHIYA: Wacce shawara za ki bai wa ‘yan’uwan ki marubuta?

RUKAYYA DANGADO: Ni shawarar da zan ba su ita ce mu rinka duba da yanayin rayuwar mu idan mun tashi rubuta littafi, mu yi rubutu mai ma’ana, kamar abin da ya shafi al’umma. Kuma kada mu yarda mu yi littafi da hankali ma ba zai dauki abin da aka rubuta ba. Ya na da kyau duk littafin da za mu yi ya zama ya na da manufa mai kyau, yadda jama’a za su sami darasi a cikin abin da su ka karanta.

(Mun ciro daga sashen Bahaushiya na cikin mujallar Fim ta watan Agusta 2017)

Loading

Previous Post

Asabe Madaki: Buri na shi ne duniya ta san ni

Next Post

Rasuwar marubuci dan kishin kasa Mahmoon Baba-Ahmed ta girgiza jama’ar Arewa

Related Posts

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro
Marubuta

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro

January 10, 2026
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama
Marubuta

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama

December 25, 2025
‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa
Marubuta

‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa

December 25, 2025
Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo
Marubuta

Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo

December 24, 2025
Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu
Marubuta

Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu

December 19, 2025
Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata
Marubuta

Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata

December 8, 2025
Next Post
Ana yi wa Alhaji Mahmmoon Baba-Ahmed Sallah

Rasuwar marubuci dan kishin kasa Mahmoon Baba-Ahmed ta girgiza jama’ar Arewa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!