• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rasuwar marubuci dan kishin kasa Mahmoon Baba-Ahmed ta girgiza jama’ar Arewa

by DAGA ABBA MUHAMMAD DA IRO MAMMAN A KADUNA
March 28, 2018
in Marubuta
0
Ana yi wa Alhaji Mahmmoon Baba-Ahmed Sallah

Ana yi wa Alhaji Mahmmoon Baba-Ahmed Sallah

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ALLAHU Akbar! Dukkan mai rai sai ya dandani mutuwa. A daren Alhamis, 9 ga Fabrairu, 2018 Allah Ya yi wa fitaccen dan jarida kuma marubucin nan Alhaji Mahmoon Baba-Ahmed, wanda ya rasu da misalin karfe 11:45 na dare a gidan sa da ke Titin Maiduguri cikin garin Kaduna, bayan ya yi fama da rashin lafiya. Baba Mahmoon, kamar yadda kowa ke kiran sa, ya rasu ya na da shekara 74 a duniya. Ya bar ’ya’ya bakwai da mata daya.

An yi masa sallah da misalin karfe 1:35 na rana, bayan sallar Juma’a a Masallacin Sultan Bello da ke Unguwar Sarki. Daga nan kuma aka wuce da shi gidan sa na gaskiya, wato makabartar da Titin Isa Kaita, a Unguwar Sarki.

Dimbin jama’ar da su ka halarci jana’izar sun hada da Alhaji Lema Jibrilu, Alhaji Umaru Mutallab, Alhaji Ahmad Maiyaki, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, Sarkin Jema’a Alhaji Muhammad Muhammad II, Ashiru Sani Bazanga, Aliyu A. Gora II, Yahaya Makaho, Dayyabu Olatunji, Jamilu Danmasukudi, Salisu Umar Salinga, Yahaya Muhammad Danhajiya, da Ahmad Yariman Tuga.



Baba Mahmoon dai ya yi fice ne a matsayin dan jarida, musamman bangaren rediyo. Ya fara aiki ne a gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna (tun ya na BCNN) a cikin 1971 a matsayin mai gabatarwa. Daga baya ya koma jaridar New Nigerian, to amma bai dade ba ya sake komawa BCNN, aka tura shi Bauchi a matsayin wakili. Daga nan ya zama wakilin gidan rediyon a jihohi daban-daban, irin su Kano, Borno, Filato da Legas.

A matsayin sa na wakili a Kano, ya yi fice saboda labaran rikicin Maitatsine da ya rika kawowa.

A shekarar 1983, Gwamna Sabo Bakin-Zuwo ya nada shi Janar Manaja na Hukumar Rediyo da Talbijin ta Jihar Kano, inda ya rike mukamin a tsawon shekara daya. Dagan an ya koma Rediyon Nijeriya na Kaduna a matsayin kwanturola mai kula das ashen al’amuran yau da kullum.



Daga baya, ya zama Daraktan Yada Labarai a Ma’aikatar Yada Labarai ta Jihar Kaduna, inda ya yi aikin shekara biyar. Daga nan aka nada shi Manajan Darakta na Hukumar Rediyo da Talbijin ta Jihar Kaduna (KSMC).

Da Alhaji Mahmoon ya yi ritaya daga aikin albashi, sai ya kafa nasa kamfanin na yada labarai, inda ya rika buga jaridar sa mai suna Garkuwa. Haka kuma ya rika rubuta filin ra’ayoyin sa mako-mako a jaridar Turanci ta Blueprint da jaridar Hausa ta Aminiya. 

Bugu da kari, ya rika gudanar da filin ra’ayoyi da kuma al’amuran yau da kullum a gidan talbijin na kannen sa, marigayi Alhaji Khalifa Baba-Ahmed da Dakta Hakeem Baba-Ahmed, wato DITV da Alheri Rediyo, kafin ya koma ya rika gabatar da filayen a gidan talbijin na Liberty da ’Yanci Rediyo inda ya rika rubuta tsokaci a kullum mai taken “Muryar ’Yanci”, wanda ake karantawa bayan labaran duniya.
Mahmoon kuma marubucin littattafai ne. 

Ya wallafa littattafan hikaya da na wasan kwaikwayo da ya rubuta da kuma fassarar wasu na William Shakespeare. Littattafan sa sun hada da ‘’Yar Halas’ da ‘Uwani Reza’. Shi ne uban kungiyar marubuta ta Alkalam da ke Kaduna.

Allah Ya jikan sa, Ya sa ya huta, amin.

Marigayi Alhaji Mahmoon Baba-Ahmed

Loading

Previous Post

Matsalar Marubuta: Mun fara gano bakin zaren, inji Rukayya Abdullahi Dangado

Next Post

Za a daura auren Sadiya Adam ran 1 ga Afrilu

Related Posts

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro
Marubuta

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro

January 10, 2026
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama
Marubuta

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama

December 25, 2025
‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa
Marubuta

‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa

December 25, 2025
Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo
Marubuta

Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo

December 24, 2025
Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu
Marubuta

Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu

December 19, 2025
Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata
Marubuta

Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata

December 8, 2025
Next Post
Za a daura auren Sadiya Adam ran 1 ga Afrilu

Za a daura auren Sadiya Adam ran 1 ga Afrilu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!