Yanzu haka dai Sadiya Adam na shirin bankwana da masana’antar shirya finafinan Hausa sakamakon auren da za ta yi a ranar Lahadi, 1 ga Afrilu, 2018.
Za a daura auren ne da wani matashi mai suna Alhaji Sanusi Ahmad (Chiroman Kasuwar Sabon Garin Kano) da misalin karfe 11:00 na safe a Masallacin Umar Bin Kattab da ke shataletalen Dangi cikin birnin Kano.
Fitacciyar jarumar dai tuni ta yi bankwana da Kannywood kamar watanni shida da su ka gabata, ta koma garin su Maiduguri da zama domin ta shirya bikin.
A da, an shirya cewar a wannan watan na Maris za a yi bikin, to sai aka samu akasi, aka dage bikin.
Wata majiyar mujallar Fim ta ce mahaifiyar Sadiyar ba ta son saurayin, shi ya sa auren bai yiwu ba.
Hakan ya sa jarumar ta dawo Kano, har ta ci gaba da wasu harkokin ta.
To sai kuma auren ya tabbata.
Sadiya Adam dai ta na daga cikin jarumai mata wadanda tauraruwar su ke haskawa a wannan lokacin.
Manyan finafinan da su ka fito da ita su ne ‘Iddah’ da kuma ‘Hasashe’ wanda ya fito kasuwa a farkon wannan shekarar.
Yanzu haka dai shiryen shiryen bikin nata sun kankama.
Amaryar da kawayen ta sun dukufa wajen dora hotunan ta tare da ango a soshiyal midiya, musamman ma Instagram, su na taya ta fatan alheri.
To Allah Ya sa a ce gara da aka yi, amin.
![]()







