BAHAUSHIYA: Da farko za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatu.
RUKAYYA DANGADO: To, assalamu alaikum. Ni dai suna na Rukayya Abdullahi Dangado. Ni haififfiyar Kano ce. An haife ni a unguwar Kantudu, Dala, shekaru 29 da su ka wuce. Na yi makarantar firamare da sakandire, daga nan kuma aka yi min aure. A yanzu ina da ’ya’ya uku, su na nan da ran su.
BAHAUSHIYA: Ya aka yi ki ka samu kan ki a harkar rubutu?
RUKAYYA DANGADO: Yadda na samu kai na a harkar rubutu shi ne, da farko ni na kasance ina sha’awar karatun littattafai tun kafin na yi aure, amma ban samu damar haka ba saboda karatu da kuma aikin gida. Amma da na yi aure sai na samu lokacin da na ke karanta littafi, kuma sai ya zama karatun littafi bai kawo min matsala da miji na ba.
To a haka ne na ga irin kokarin da marubuta su ke yi na fadakarwa da ilimantarwa. Wannan shi ne ya ja hankali na na fara rubuta littattafai. Ga shi kuma har Allah Ya kawo mu lokacin da ake damawa da mu.
BAHAUSHIYA: A wacce shekara ki ka fara fitar da littafi?
RUKAYYA DANGADO: Na fara fitar da littafi a 2006; kuma littafi na da ya fara shiga kasuwa a lokacin shi ne ‘’Yar’uwa Ko Kishiya?’
BAHAUSHIYA: Wanne littafi ne ya fito da ke aka san ki a matsayin marubuciya?
RUKAYYA DANGADO: Littafin dai da na fara yi ‘’Yar’uwa Ko Kishiya?’ shi ne ya fito da ni, domin ya samu karbuwa duk da ina sabuwa a lokacin, don haka shi ne ya jawo min daukaka a wajen masu karatu. Na gina labarin ne a kan zamantakewar uwargida da abokiyar zaman ta da kuma yaran da su ka haifa. To na kawo darasi a kan yadda ya kamata su zauna, da kuma nuna cewar zuwa wajen boka ba ya kawo ci-gaba a rayuwa, a fuskanci gaskiya da rikon amana.
BAHAUSHIYA: Zuwa yanzu littattafan da ki ka yi za su kai kamar nawa?
RUKAYYA DANGADO: A yanzu dai littattafan da na yi sun kai guda goma, su ne kamar haka: ‘’Yar’uwa Ko Kishiya?’, ‘Menene Matsayi Na?’, ‘Aure Na Jari Na’, ‘Yaya Zan Yi Da Rashin Gata?’, ‘Hudubar Shaidan’, ‘Kuka Ya Zama Dole’, ‘Ban Yi Wa Kai Na Adalci Ba’, ‘Zaluncin Kauna’, ‘Ishara’, ‘Wa Zai So Ni?’
BAHAUSHIYA: Wane littafi ki ka fi so a cikin littattafan ki?
RUKAYYA DANGADO: To, littafin da na fi so a cikin littattafai na shi ne ‘Ishara’. Ina son sa ne ba don komai ba sai yadda salon labarin ya bambanta da sauran wadanda na rubuta, musamman yadda na bata tsawon lokaci har kusan shekara ina rubutun sa, sabanin sauran da ba na daukar lokaci na ke gamawa. Don haka sai salon sa ya zo da jan hankalin mai karatu.
BAHAUSHIYA: Wadanne irin matsaloli ki ke fuskanta a harkar rubutu?
RUKAYYA DANGADO: Matsaloli kam an fuskance su, don ba za a ce babu ba, musamman yadda kasuwar littafin ta ke. Ka san kukan marubuta kullum a kan ’yan kasuwa ne, yadda su ke rike mana kudi, kuma ba wai don ba a sayar ba ne, kawai dai fitowar kudin ce ta ke zama wahala, don kafin su fita sai an kai ruwa rana. Amma dai yanzu mun fara gane bakin zaren wajen dakatar da duk wanda bai biya kudi ba, to ba za mu ba shi kaya ba.
BAHAUSHIYA: Wadanne irin nasarori ki ka samu a harkar littafi?
RUKAYYA DANGADO: Ina godiya ga Allah don na samu nasara ta bangarori daban-daban. Littafi ya kara daga daraja ta fiye da yadda ba na zato. Ina jin dadi a duk lokacin da na ga masoya na masu karatun littafi na.
BAHAUSHIYA: Wacce shawara za ki bai wa ‘yan’uwan ki marubuta?
RUKAYYA DANGADO: Ni shawarar da zan ba su ita ce mu rinka duba da yanayin rayuwar mu idan mun tashi rubuta littafi, mu yi rubutu mai ma’ana, kamar abin da ya shafi al’umma. Kuma kada mu yarda mu yi littafi da hankali ma ba zai dauki abin da aka rubuta ba. Ya na da kyau duk littafin da za mu yi ya zama ya na da manufa mai kyau, yadda jama’a za su sami darasi a cikin abin da su ka karanta.
(Mun ciro daga sashen Bahaushiya na cikin mujallar Fim ta watan Agusta 2017)
![]()







